01/05/2026
JUM’AT MUBARAK 🌙🤲
Da fatan kowa yana cikin koshin lafiya da rahamar Allah, da jinkansa, da kaddararsa, da taimakonsa.
Muna miƙa godiya ta musamman ga dukkan shugabanni (Stakeholders) da kuma jam’iyyar APC baki ɗaya bisa amincewa da tsayar da
HON. TUKUR YUSUF DADDY a matsayin ɗan takarar sulhu (Consensus Candidate) na Majalisar Jiha, Funtua LGA.
Wannan matsaya ba ƙaramin nasara bace ga al’ummar Funtua, musamman matasa masu burin ganin canji na gaskiya.
Lokaci ya yi da matasnmu zasu samu dama kuma mafarkinsu zai Ƙarfa'fa, kuma harkar noma zata Farfaɗo domin cigaban al’ummar garin Funtua da kewayenta.
Hon. Daddy mutum ne mai matukar hangen nesa, kuma wannan dama ce ta gina Funtua mai ƙarfi tareda gudunmawar kowa a garin Funtua.
Muna godiya ƙwarai da gaske ga kowa da kowa da ya bada gudunmawa wajen wannan matsaya. Allah ya saka da alheri.