09/07/2023
BANKWANA DA JINJINA GA MALAM ABDULSHAHID MAHMUD INUWA FASKARI.
A LONG TIME SERVING CHAIRMAN OF FASKARI YOUTH FOUM( FYF) TAREDA TAYA MURNA GA SABBIN JAGORORI.
A watannin baya da s**a gabata, wakilai daga cikin qungiyar dalibai matasa ta Faskari wato Faskari young students orientation forum_ FYSOF. Karkashin jagorancin Cmrd Aliyu Tukur Faskari ta samu kai ziyarar taya murnar aure ga shugabanmu, Malaminmu, kuma Yayanmu tsohon shugaban FYF a gidanshi dake a Faskari, bayan sati daya dayin aure, ana daf da yin manyan zaɓuka na shugabancin Nigeria kasarmu.
Mun tattauna abubuwa da dama sosai, cikin raha da annashuwa haka shugaba ya tarbe mu.
Abubuwan da muka tattauna sun haɗa da:
1. Tarihin ita kanta Babbar ƙungiya(FYF)
Wannan ya haɗa da yadda aka kafa ta, da shugabancin ta tun daga ranar farko har zuwa yanzu, kalubalen da aka fuskanta wajen gudanarwa, nasarorin da aka samu wajen gudanarwa, da kuma abubuwan da ƙungiyar taso ta aiwatar wadanda Allah be basu dama ba har zuwa yanzu. Amma in Sha Allah har yanzu kada a fidda ran cimma wannan.
2. Shawarwari ga Faskari Young students orientation forum akan yadda zamu ɓullo ma cimma muradanmu muma.
Kasancewar FYF madubi ga FYSOF, mun dauki alkawarin in sha Allah zamu cigaba da bibiya da bin hanyoyin nasarori da kuma shawari daga manya a cikin FYF domin kawo ma gari cigaba.
3. Makomar matasan karamar hukumar mu ta Faskari a siyasance.
4. Da dai sauran abubuwa masu muhimmanci waɗanda Lokaci baze bari a lissafo su ba.
Muna rokon Allah ya saka ma tsofaffin shuwagabannin kungiyar FYF da alkhairi bayan shafe shekaru 10 suna shugabantar kungiyar, kuma alhamdulillah sun riketa cikin aminci da amana, kuma sun riketa da ƙudiri na ci gaba, shiyasa Allah ya taimakesu a lamurran tun daga farko har karshe.
Fatan alkairi ga Sabbin jagororin wannan ƙungiya me son cigaban al'umma.
Fatan alkhairi ga wadanda s**a dade suna bada gudunmawa ga cigaba.
Fatan Alkhairi ga Dahiru Inuwa da muƙarrabanshi.
AbdulShahid Mahmud
Ahmad A Bawa Faskari
Auwal Badaru
Isyaku Wada Faskari
Sabakiyu Abubakar
Da sauran wadanda basu anbatu ba, FYSOF na maku fatan alkairi.