15/09/2025
"Wasu suna yawan cewa 'sabani tsakanin malamai rahama ne', amma gaskiya malamai sun bayyana cewa wannan magana bata tabbata daga Annabi ﷺ ba. Sheikh Ṣāliḥ al-Fawzān yace: sabani ba rahama ba ne, rahama tana cikin hadin kai da bin gaskiya. Allah ma ya ce: 'Zasu ci gaba da yin sabani, sai waɗanda Ubangijinka ya yi musu rahama' (Hud: 118-119).
Don haka mu mai da hankali wajen bin gaskiya da nassin da ya tabbata, mu guji amfani da kalmomi marasa tushe."