SA'IN Birnin KUDU Foundation

SA'IN Birnin KUDU Foundation Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from SA'IN Birnin KUDU Foundation, Nonprofit Organization, Birnin Kudu Local Government, Birnin-Kudu.

A yaune  ranar Alhamis 15/01/2026 da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, Gidauniyar SA'IN BIRNIN KUDU ( SA'I Foundation) ta kai...
15/01/2026

A yaune ranar Alhamis 15/01/2026 da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, Gidauniyar SA'IN BIRNIN KUDU ( SA'I Foundation) ta kai ziyara zuwa Makarantar Sakandaren Arabiya ta Kwana dake Katafilu, Birnin Kudu domin gabatar da lakca akan tsaftar muhalli da tsaftar jiki.

Manufar wannan ziyara ita ce wayar da kan ɗalibai game da muhimmancin tsafta wajen kare lafiya da kuma hana yaduwar cututtuka a cikin makaranta da al’umma baki ɗaya.

A yayin lakcar, an yi bayani dalla-dalla kan abinda ya shafi

1.Muhimmancin tsaftace muhalli kamar ɗakunan kwana, azuzuwa da bandakuna
2.Amfanin tsaftar jiki kamar wanke hannu, tsaftace kaya da jiki akai-akai
3.Illolin rashin tsafta ga lafiya da karatu
4.Rawar da ɗalibai za su taka wajen kiyaye tsafta a makaranta da gida

Ɗalibai sun nuna farin ciki da kulawa sosai, tare da amsa tambayoyi da kuma bayar da gudunmawa a tattaunawar. Hakan ya nuna cewa sun fahimci sakon da aka isar musu.
Gidauniyar SA'IN BIRNIN KUDU ta jaddada aniyarta na ci gaba da shirya irin wannan shirye-shiryen domin tallafa wa cigaban ilimi, lafiya da tarbiyyar matasa a cikin al’umma.

Allah ubangiji yasa su amfana da ilimin da s**a koya Kuma Suma su amfanar shi ga wasu.

Maga takardar Gidauniya
Mubarak Ibrahim.

Address

Birnin Kudu Local Government
Birnin-Kudu

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SA'IN Birnin KUDU Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share