Birnin-kudu city

Birnin-kudu  city Birnin-kudu is a town and a local governmen t area in south of jigawa state nigeria. some 120 kilometres in the south-east of kano state.

26/05/2026
INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN.Jama’a ba mutuwa akayi ba, muna tuna irin muwuyachi halin matsi da al’umar mu suke cik...
24/05/2026

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN.

Jama’a ba mutuwa akayi ba, muna tuna irin muwuyachi halin matsi da al’umar mu suke ciki ne, gashi Sallah tana tunkaro mu kuma ruwan famfo ma wadda za’ayi wankan sallah da sauran hidimomi ya gagara.

Birnin kudu akwai korafi.
Birnin Kudu babu ruwa.
Birnin Kudu muna bukatar adalchi.

Kuma abun kullum yana kara ta’azzara amman sunyi ko in kula da bukatar talakawa😭😭😭

🚨 KIRA NA GAGGAWA DOMIN CETON RAYUKAN MATAFIYA DA MAZAUNA MASAYA, BIRNIN KUDU 🚨Wannan saƙo ba na siyasa ba ne, kira ne n...
12/05/2026

🚨 KIRA NA GAGGAWA DOMIN CETON RAYUKAN MATAFIYA DA MAZAUNA MASAYA, BIRNIN KUDU 🚨

Wannan saƙo ba na siyasa ba ne, kira ne na tausayi da kishin rayukan al’umma.

Babban titin gwamnatin tarayya da ya haɗa jihohin Kano – Bauchi – Gombe – Taraba – Adamawa, musamman ɓangaren Masaya da ke ƙaramar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa, ya lalace matuƙa har ya kai matsayin da yake dab da katsewa gaba ɗaya.

A kullum dubban matafiya, direbobi, ‘yan kasuwa da marasa lafiya ne ke amfani da wannan hanya. Amma abin takaici, titin yanzu ya zama barazana ga rayuka da dukiyoyi saboda tsananin lalacewa.

Muna kira cikin girmamawa ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta ɗaukar mataki kafin wani mummunan haɗari ya afku:



(FERMA)

'Forum





Gyaran hanya kafin bala’i ya faru shi ne alamar shugabanci nagari da kula da rayuwar jama’a.

Allah Ya kare rayukan matafiya, Ya sa a ɗauki mataki cikin gaggawa. Ameen. 🤲

AN BADA IZININ FARA BINNEWA A SABUWAR MAƘABARTAR BITINARIYA💔Alhamdulillah, an kammala gyara da sharewa maƙabartar Bitina...
09/05/2026

AN BADA IZININ FARA BINNEWA A SABUWAR MAƘABARTAR BITINARIYA💔

Alhamdulillah, an kammala gyara da sharewa maƙabartar Bitinariya Birninkudu, kuma daga yanzu an amince da fara binnewa a cikinta cikin tsari mai kyau da tsafta.

An tsara wajen ta yadda za’a samu sauƙin zirga-zirga da kiyaye martabar maƙabarta, inda aka tanadi:

✅ Layin Manya
✅ Layin Yara
✅ Hanyoyin Wucewa
🚺Sannan ga Alamomi (Symbols) domin nuna tsari.

🙏 Don Allah muna roƙon al’umma da duk masu zuwa maƙabartar da su kiyaye wannan tsari domin dorewar tsafta da mutuncin wajen.

🤗Haka kuma muna miƙa saƙon godiya da jinjina ga ɗaukacin al’umma, waɗanda s**a halarta wajen aikin sharewa da gyaran maƙabartar, da kuma masu bayar da gudummawa ta kuɗi, ƙarfi, da shawarwari. Tabbas an nuna haɗin kai da ƙoƙari mai girma.

🤲 Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka wa kowa da alkhairi, Ya sanya wannan aiki a ma’aunin ayyukan alheri, Ya gafarta wa mamatanmu baki ɗaya. Amin.

✍️ Daga:
Kwamitin Kula da Hidimtawa Maƙabartar Rashen Bitinariya Birninkudu (BILOCPA)

Site View of Birnin kudu tonight🌃
04/05/2026

Site View of Birnin kudu tonight🌃

BIRNIN KUDU A HALIN YANZU.
19/04/2026

BIRNIN KUDU A HALIN YANZU.

KOFAR SARKIN KUDU ALH HASSAN JIBRIN
03/04/2026

KOFAR SARKIN KUDU ALH HASSAN JIBRIN

Somewhere in Birnin Kudu.
02/04/2026

Somewhere in Birnin Kudu.

Address

Maiduguri Road
Birnin-Kudu

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Birnin-kudu city posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share