11/08/2025
HADIN KAN MATASA A ALIERO QUARTERS (KASHI NA DAYA)
Aliero Quarters unguwace acikin garin Birnin Kebbi, Kebbi State, under Gwadangaji ward, samada shekara 20 Ayau mutane na rayuwa acikinta.
Samun Hadinkai Yana daya daga cikin manyan manufofin masu kishin cigaba a Aliero Quarters.
Tabbas Duk lokacinda kaga cigaba to akwai alamun karuwar haɗin Kai acikin al'umma.
Zanyi magana gameda wata muhimmiyar kungiyar Matasa Wadda wasu matasa s**a kafa don bada tasu gudunmuwa acikin wannan unguwa Aliero Quarters.
Wannan Kungiyar itace:
ALIERO ESTATE YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION (AEYDA)
Wannan Kungiya Tayi abin ayaba Kuma ajinjina domin kuwa tadauki hanyar tsaftace unguwa wato monthly sanitation Wanda Yana daya daga cikin abubuwa mafi muhimmanci acikin kowace Al'umma shine tsafta.
Haka zalika wannan Kungiya tadauki hanyar yin renovation na wurare daban daban acikin unguwa inda tafara da Canza Fentin Main-Gate na Aliero Quarters.
Haka zalika tana gyara kananan matsalolin da s**a faru domin cigaban Al'umma kamardai gyaran fanfo idan ya lalace kokuma Saka masa siminti domin inganta wurare acikin unguwa.
Wannan Kungiyar tasamu gudunmuwar Al'umma ta6angarori daban daban, kadan daga ciki akwai Yahaya Sarki (special adviser to the executive government S.A media), Daudu Prince, Justice Maryam Hassan Kaoje, Malam Nasiru Kigo, Abubakar Ahmad Raba, Alhaji Aminu Abdullahi (Chairman Board Of Internal Revenue), Hajiya Nafisa salihu bagudo (Mai bada shawara ta musamman ga Matar Gwamnan Jahar Kebbi).
Akwai mutane da kungiyoyi wadandama Ba'a ambataba, musamman wadanda s**a taimaka da shawarwari har zuwa cinma wannan nasara kamardai kungiyar Matasa da sauran Malamanda s**a gudanarda Lecture agurin Wa'azinda akayi cikin Ramadan.
Kungiyar na bukatar Taimakon masu hannu da shuni don cigaba da gudanarda wasu ayyuka dasufara.
Tabbas baza'a rasa matsaloliba tattare da wannan Kungiya, Ammadai komenene sunyi abin koyi Kuma abin ayaba dabakowa zai iyaba.
Mutaimaki Irin wadannan kungiyoyin Koda kuwa da yada abubuwanda sukeyine domin karamasu Kwarin guiwar cigaba da Aiki don kawoma unguwa cigaba.
Manta da Tarin manufofinda bakada tabbas na 'yan Kungiya, fuskanci cigabanda suke iya kawowa, dahaka ake Samun cigaba akowace Al'umma.
Allah yasakama kowa da Alkhairi, Ameen.
Allah yadaga wannan Kungiya,
Allah yadaga Aliero Quarters,
Allah yadaga Birnin Kebbi,
Allah yadaga Kebbi State,
Allah yadaga Nigeria.