Kebbi State Quranic Recitation Competition

Kebbi State Quranic Recitation Competition This is Official page of Kebbi State Quranic Recitation Competition Musabaqah (Social media).

01/08/2026

Masha Allah

Musabaqar Alƙur'ani ta Duniya Ta maleek Abdul-Aziz karo na 46.Mai Girma Ministan Harkokin Addinin Musulunci, kuma Babban...
31/07/2026

Musabaqar Alƙur'ani ta Duniya Ta maleek Abdul-Aziz karo na 46.

Mai Girma Ministan Harkokin Addinin Musulunci, kuma Babban Mai Kula da Musabaqoqin Alƙur'ani na Cikin Gida da na Ƙasa da Ƙasa, Sheikh Dr. Abdul Latif bin Abdulaziz Al Alsheikh, ya ƙaddamar da sabon mataki tare da jagorantar gudanar da Gasar Alƙur'ani ta Ƙasa da Ƙasa ta Sarki Abdulaziz karo na 46, wadda ta haɗa da haddar Alƙur'ani, kyakkyawar tilawa ,tafsiri da kira'at.

Za a gudanar da gasar daga 23 ga Safar zuwa 6 ga Rabi'ul Awwal 1448H.

A bana, gasar ta kafa sabon tarihi inda mahaddata maza da mata 334 daga ƙasashe 133 na duniya za su halarta, lamarin da ya sa wannan ita ce mafi girman gasar tun bayan kafuwarta, bisa yawan mahalarta da ƙasashen da s**a samu wakilci.

Allah yabaiwa Nigeria 🇳🇬 nasara Amen.

30/07/2026
30/07/2026

BASHIR ABUBAKAR MUHAMMAD BORNO STATE 30 HIZB

28/07/2026

Alhmamdulillah it's now Official

Musabaqar Bana Jigawa Daga ranar 14/11/2026 zuwa 30/11/2026 In Sha Allah

Sanarwa
28/07/2026

Sanarwa

27/07/2026

Masha Allah �

Da Ɗumi-Ɗumi | An Buɗe Gasar Karatun Alƙur'ani ta Jihar Borno Karo Na 41(1448AH/2026) A HukumanceA wajen bikin buɗe gasa...
26/07/2026

Da Ɗumi-Ɗumi | An Buɗe Gasar Karatun Alƙur'ani ta Jihar Borno Karo Na 41(1448AH/2026) A Hukumance

A wajen bikin buɗe gasar da aka gudanar a yau lahadi 26 July,2026, Shugaban Hukumar Shirya Gasar Karatun Alkur'ani, Khalifa Aliyu Ahamed Abulfathi, ya gabatar da jawabin maraba.

Haka shi ma sakatare na Majalisar Alƙur'ani, Shaikh Tijjani Umara, ya gabatar da nasa jawabi, yayin da Shugaban Taron kuma Kwamishinan Ilimi na Jihar Borno, Injiniya Lawan Abba Wakilbe, wanda Dr. Abba Mala, daraktan harkokin makarantu na ma'aikatar Ilimi ya wakilta, ya gabatar da jawabi a madadinsa.

Ma’abota littafin Allah Ababen Koyi 🤎💙Ku fada mana kalma daya tak game dasu…?
25/07/2026

Ma’abota littafin Allah Ababen Koyi 🤎💙

Ku fada mana kalma daya tak game dasu…?

Alhamdulillah! An gudanar da rufe Musabaƙar Alƙur'ani Mai Girma ta Jihar Jigawa karo na 41 na shekarar 2026, inda cikin ...
24/07/2026

Alhamdulillah! An gudanar da rufe Musabaƙar Alƙur'ani Mai Girma ta Jihar Jigawa karo na 41 na shekarar 2026, inda cikin ikon Allah aka fitar da Gwarzo da Gwarzuwa na jihar tare da sauran waɗanda s**a yi fice a fannoni daban-daban na gasar.

Haka kuma, da yardar Allah, ana sa ran Musabaƙar Alƙur'ani ta Ƙasa (National Musabaqa) ta shekarar 2026 za a gudanar da ita ne a Jihar Jigawa, inda za ta haɗa mahalarta daga dukkan jihohin Najeriya domin fafatawa a wannan gagarumar gasa ta Alƙur'ani, In shaa Allah.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya kaimu wannan lokaci cikin ƙoshin lafiya, Ya ba da ikon halarta, Ya sanya ta zama mai albarka ga al'ummar Musulmi baki ɗaya.

Allah Ya ƙara ɗaukaka Alƙur'ani, Ya albarkaci malamai, alƙalai, iyaye, masu shirya wannan gasa, da dukkan mahaddata. Ya sanya Alƙur'ani ya zama jagoran rayuwarmu a duniya, haske a kabarinmu, kuma mai ceto gare mu a ranar Alƙiyama. Āmīn. 🤲

📷: Kamaludeen Abubakar


Address

Birnin-Kebbi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kebbi State Quranic Recitation Competition posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Kebbi State Quranic Recitation Competition:

Shortcuts

Share