First Aid Group of Jibwis Bichi Division

First Aid Group of Jibwis Bichi Division This is the Only Official page of First Aid Group of Jibwis Bichi Division, Kano State.

FIRST AID GROUP OF JIBWIS BICHI DIVISION ZIYARAR TA'AZIYYAHTawagar Daraktan Agaji na Jahar Kano Mal. Mukhtar Lawan Tudun...
03/10/2026

FIRST AID GROUP OF JIBWIS BICHI DIVISION

ZIYARAR TA'AZIYYAH

Tawagar Daraktan Agaji na Jahar Kano Mal. Mukhtar Lawan Tudun Wada ta kai Ziyarar Ta'aziyyar rasuwar Mal. Imam Adam Mataimaki na Biyu ga shugaban JIBWIS na Bichi.
Daraktan ya gabatar da Addu'o'i haɗe da nasihohi ga iyalan Marigayi Mal. Imam

Muna Addu'a Allah ya yi ma Mal. Imamu Rahma.

A ƙarshe muna Addu'a Allah yasaka ma Darakta da Alkhairi yamai dashi gida lafiya.
✍️Sadeeq Muhammad
Divisional Publicity Secretary

SAƘON TA'AZIYYAMajalissar Agaji ta Bichi ƙarƙashin jagorancin Mal. Lukman Muhammad Ahmad ta na miƙa saƙon ta'aziyyah zuw...
01/10/2026

SAƘON TA'AZIYYA

Majalissar Agaji ta Bichi ƙarƙashin jagorancin Mal. Lukman Muhammad Ahmad ta na miƙa saƙon ta'aziyyah zuwa ga Mal. Ridwan Sulaiman Zarewa bisa Rasuwar Ɗan sa Sabeer.

Muna Addu'a Allah ya Yi masa Rahma ya bada Haƙurin Rashin Sa.

إِنَّ لِلَّهِ مَا أَخَذَ، وَلَهُ مَا أَعْطَى، وَكُلُّ شَيْءٍ عِنْدَهُ بِأَجَلٍ مُسَمًّى، فَلْتَصْبِرْ وَلْتَحْتَسِبْ.الل...
30/09/2026

إِنَّ لِلَّهِ مَا أَخَذَ، وَلَهُ مَا أَعْطَى، وَكُلُّ شَيْءٍ عِنْدَهُ بِأَجَلٍ مُسَمًّى، فَلْتَصْبِرْ وَلْتَحْتَسِبْ.

اللَّهُمَّ اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، وَعَافِهِ وَاعْفُ عَنْهُ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ
Cikin Alhini da jimami Shugaban Majalissar Agaji ta Karamar Hukumar Bichi yana mika sakon Ta'aziyya ga iyalai da sauran Musulmin duniya Baki daya Bisa Rasuwar Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Izala na 2 na karamar Hukumar Bichi Mal. Imam Adamu. Allah ya jikansa ya gafarta masa ya kyautata makwancinsa. Da sauran Musulmi Baki daya.

Amadadin

Mal. Lukman Muhammad Ahmad
Divisional Leader
FAG OF JIBWIS Bichi Division

FIRST AID GROUP OF JIBWIS BICHI DIVISIONSAƘON TAYA MURNAMajalissar agaji ta Bichi Ƙarƙashin Jagorancin Mal. Lukman Muham...
25/09/2026

FIRST AID GROUP OF JIBWIS BICHI DIVISION

SAƘON TAYA MURNA

Majalissar agaji ta Bichi Ƙarƙashin Jagorancin Mal. Lukman Muhammad Ahmad tana taya Dr. Sadeeq Muhammad (Div. Publicity Secretary) Murnar Rantsar da shi a Matsayin Cikakken Likitan Ido daga Jami'ar Bayero dake Kano.

Muna Addu'a Allah Ya sanya Albarka.

First Aid Group of Jibwis Bichi Division Media Team

FIRST AID GROUP OF JIBWIS BICHI DIVISION, KANO STATESAKON TAYA MURNA! Alhamdulillah, Majalissar Agaji ta Bichi ƙarƙashin...
23/09/2026

FIRST AID GROUP OF JIBWIS BICHI DIVISION, KANO STATE

SAKON TAYA MURNA!

Alhamdulillah, Majalissar Agaji ta Bichi ƙarƙashin Jagorancin Mal. Lukman Muhammad Ahmad ta na taya Mal. Sulaiman Muhammad Ahmad wanda Shine Divisional Commandant na Bichi Murnar Samun Scholarship Zuwa ƙasar Malaysia Domin Yin Degree na Biyu(2).

Muna Addu'a Allah Ya kaishi Lafiya, ya bashi nasara ya dawo mana da shi lafiya.

✍️ First Aid Group of Jibwis Bichi Media Team.

Sanarwar Ga Jama'a Asabar 30 Rabi'ul Auwal / Saturday 12 Sep, 2026Sheikh Dr Kabir Gombe Ya Gwangwaje Daraktan Agajin Kan...
12/09/2026

Sanarwar Ga Jama'a
Asabar 30 Rabi'ul Auwal / Saturday 12 Sep, 2026

Sheikh Dr Kabir Gombe Ya Gwangwaje Daraktan Agajin Kano Da Kujerar Aikin Hajjin Bana

Majalisar Agajin Izalar Kano karkashin jagorancin Daraktan Agajin Izala na jihar Kano Malam Mukhtar Lawan Tudun Wada ta mika sakon godiya ta musamman ga babban sakataren kungiyar Izala na tarayyar Najeriya Sheikh Dr Muhammad Kabir Haruna Gombe (Maddibon Lau) bisa Gwangwaje Daraktan Agajin Kano da kujerar aikin Hajjin bana 1448/2027 da yayi.

Shehin Malamin na kokari sosai wajen hidimtawa yan Agaji musamman a fadin jihar kano dama kasa baki daya duba da yadda yake basu tallafin kayan abinci akai akai da kuma sama musu abubuwan more rayuwa da kayayyaki domin gudanar ayyukan Agaji a lunguna da sako da sassan kasa baki daya.

Daga karshe majalisar tayi addu'a ta musamman ga shehin malamin da kuma shugaban kungiyar na tarayyar Najeriya Sheihk Dr Abdullahi Bala Lau.

Allah Ya Karawa Rayuwarsu Albarka,
Allah Ya Kara Taimakon Izala
AMEEN.

Sanarwa:
DSP A. Bello
Babban Jami'i,
Sashen Yaɗa Labarai Da Hulɗa Da Jama’a Na
Majalisar Agajin Izala Ta Jihar Kano.

09/09/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Ishaq M B*h, Fatima Hassan, Uthman Rabiu Usee, A S Bako Bichi, Abubakar Kabiru Abubakar, Abubakar Ibrahim, Adamu Dan Takai, Musa Muhd, Abubakar G. Buhari, Sojan Sunnah, Sp Alaj Zarewa, M Jee Ka, Yasir M Gyada, Baheejjat Abdullahee, Ahmerd Ameen Bichi

Tawagar Majalisar Agajin Izalar Kano Karkashin Daraktan Agajin Izala Na Jihar Kano Malam Mukhtar Lawan Tudun Wada Takai ...
28/08/2026

Tawagar Majalisar Agajin Izalar Kano Karkashin Daraktan Agajin Izala Na Jihar Kano Malam Mukhtar Lawan Tudun Wada Takai Ziyayar Dubiya Gidan Malam Abdulmajid Yakubu Bichi Domin Duba Lafiyarsa.

Malam Abdulmajid Yakubu Bichi (Tsate Operation Officer) Ya Samu Iftila'in Hadarin Mota A Hanyarsu Ta Zuwa Samina/Kamfin Na Yan Agajin Izala Daya Gudana A Jihar Bauchi A Shekarar 2024.

Tawagar Data Kunshi Malam Aliyu Kwara (National Traffic Officer) Yan Agajin Jihar Kano (State Members) Da Yan Agajin Karamar Hukumar Fagge (Divisional Members)

Majalisar Ta Mika Tallafin Abinci Da Kudi Ga Majinyacin Domin Rage Masa Radadi.

Allah Ya Kara Masa Lafiya.
AMEEN.

✍️ Abubakar Bello (DSP A. Bello)
Kano State Publicity Secretary
28 Juma'a, 2026AH.

KUSAN FUSKOKIN YAN AGAJIN KU NA BICHIMeet Engr Abdullahi Sunusi Bako , Former President National Association of Bichi St...
28/08/2026

KUSAN FUSKOKIN YAN AGAJIN KU NA BICHI

Meet Engr Abdullahi Sunusi Bako , Former President National Association of Bichi Students ( F. C. E Bichi chapter),a young man who devoted his time to serving islam through First Aid Group of JIBWIS.

Year of Enrollment: 2009
Rank: Divisional Treasurer

Educational Background:
Federal college of Education Technical Bichi - N. C. E

Government Technical College Ungoggo - SSCE

Bichi Educational Foundation - JSCE

Umar Bn Khaddab Nursery and primary School Bichi - First Leaving Certificate

Training and Certifications:
-Council for the Regulation of engineering in Nigeria (COREN)
-Teachers Registration Council of Nigeria

Working Experience:

-Teaching practice at Government Technical College bichi
-Class Room Teacher at Usman bn Affan Islamiyyah Bichi
- Currently working at SIB investment.

Skills:

Welding and Fabrication.

BICHI A&B DETACHMENT CAMPING 2026 Alhamdulillah, Jiya Laraba 26-08-2026 an kammala Detachment Camping da aka Shirya ƙarƙ...
27/08/2026

BICHI A&B DETACHMENT CAMPING 2026

Alhamdulillah, Jiya Laraba 26-08-2026 an kammala Detachment Camping da aka Shirya ƙarƙashin Jagorancin Shugaban Majalisar Agaji ta Bichi Mal. Lukman Muhammad Ahmad Wannan Camping an gudanar da shi a Masallacin Juma'a na Abubakar Mahmoud Gumi Bichi na tsawon kwanaki Uku.

Mal. Sulaiman Muhammad Ahmad (Divisional Commandant, Instructor Grade II) Abbas Salisu Hassan (Deputy Divisional Commandant), Suhaibu Khamilu ( Assistant Divisional Commandant) Sune S**a Jagoranci Training ɗin da sauran Baƙin da s**a taya su Aiki, Daga F. C. E. Detachment.

Allah Ya saka Musu Da Alkhairi da sauran waɗanda s**a jajirce a wurin Wannan Camping ɗin.

A ƙarshe, a Madadin Shugaba Mal. Lukman Muhammad Ahmad Muna wa kowa ban gajiya tare da Fatan Kowa Ya Koma Gida lafiya.

Photo: Engr Abdullahi Sunusi Bako & Aliyu Ahmad Nalado
✍️ Muhammad Shafeeu Muhammad
Deputy Divisional Secretary
Member First Aid Group of Jibwis Bichi Media Team.

Address

Tsohuwar Tasha
Bichi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when First Aid Group of Jibwis Bichi Division posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to First Aid Group of Jibwis Bichi Division:

Shortcuts

Share