05/05/2026
NASIHA GA IYAYE MAZA DA MATA AKAN AURE
*************************************
BURIN MACE KO NAMIJI GAMEDA ABOKIN RAYUWAR AURE
Kowace macen da ta kai minzalin aure, ƙololuwar burin ta a rayuwa shine taga ta auri mutumin kirki wanda yake kwatanta koyi da tafiya bisa tafarkin Manzon Tsira SAW., Wanda take sa ran zai kwatanta yi mata adalci da kyautata muamala gareta a yayin su ka yi aure.
To amma son hakan a zuci ko kuma faɗar sa da baki kaɗai ba zai isa ba wajen samun cikar wancan burin nata matsawar dai ba ta haɗa da aiki tuƙuru bisa juriya da jajircewa ba.
A matsayin ki ta mace, koda ace kin yi sa'a Allah ya azurta ki da irin wancan abokin zaman da k**e buƙata, to fa sai kin yi aiki tuƙuru kafin ki iya tatsowa da canjawa ko ɗora wannan miji naki bisa turbar da wannan auren naku zai bunƙasa har ya kai ga nasarar da k**e buƙata.
Kisa aran ki cewa ba zaki taɓa samun abinda k**e so daga wajen mai gidan ki ba har sai kin zauna kinyi sabon karatu mai zurfi akan sa yadda zaki masa fahimta irin ta ciki da waje, kuma irin wannan karatu ya sha bambam da duk wanda kika yi masa a baya kafin ku yi aure, domin duk yadda k**e tsammanin kin shaƙu dashi saboda kusanci na soyayya data gabata kafin aure, to daga sanda aka ɗaura aka shigo gida, to fa karatu ya dawo sabo, ki ƙaddara cewa a baya baki san shi ba yanzu ne zaki san ainifin waye shi.
Da zarar kin fahimci irin kalar mai gidan naki, ba tare da wata-wata ba sai ki ɗaura ɗammarar yin aiki na fuskantar ƙalubalen da ke gabanki manya da ƙanana.
Misali:
Akwai buƙatar ki zamo mai nuna wa mai gidan ki kulawa cikkakka, mai ƙara masa ƙwarin guiwa, mai taimakon sa bisa sauke nauyin da ke kan sa, mai riƙe asirin sa, kana mai miƙa masa yarda da amincin ki.
Akwai buƙatar ki zamo mai yawan murmushi (haƙiƙa shi babban makami ne dake cin zukatan mazaje da yaƙi), mai yin ba'a (wasa) da dariya, mai shagwaɓa, wani lokacin kuma ki zamo kece mai lallashi/rarrashi,.
Akwai buƙatar ki zamo mai nuna masa cewa da gaske fa kina SON shi (irin huɗubar nan da akewa yaran mata cewa ba'a nunawa miji soyayya ko sakin jiki dashi saboda ba ɗan goyo ba ne, huɗuba ce ta shaiɗan ki nisance ta), ki zamo tushen samuwar nutsuwa, farin ciki da kimtsuwar sa, ki nuna masa cewa baki da wani abu a duniya daya kai muhimmancin sa agareki; ya fi miki tarin dukiya da duk wani ƙyale-ƙyalen duniyar nan.
Ki zamo masa MACE a aikace ba a suna ba ta hanyar amfani da baiwar da Ubangiji yai miki na halitta don samarwa mijin nutsuwa wanda kuma shine ya bambamta ki da namiji (Akwai matan da sunan mata kawai suke amsawa amma duk muamalar su irin ta maza ne, irin waɗannan matan ba yadda za'ayi su iya nasarar kame zukatan mazajen su, saboda shi namiji da mace yake buƙatar zaman aure ba macen-namiji ba).
Ki zamo mai lura da ƙarfafar tunanin sa da motsin ruhin sa ta kowane irin yanayi na ɓacin rai ko annashuwa, ki zamo mai haƙuri da juriya wajen ɗaukar ɗawainiyar sa, mai ƙarfafa shi cikin gyaran alaƙar sa da Ubangijin sa, ki taimake sa wajen riskar ƙololuwar matsayi na zamowa cikin sahun cikakkun bayin Allah masu biyayya.
IN MUKA KOMA ƊAYA GEFEN KUMA:
Suma maza kowannen su burin sa shine ya auri mace wacce take kan tafarkin koyi da Sayyidah Khadija (r.t.a) wanda kowa yasan irin kulawar da ta bawa Manzo SAW. ne hakan ya bata babban matsayin da bama ita ba hatta ƙawayen ta Manzon Allah SAW yana girmama su da wani irin girma na musamman.
To amma shima namiji kamar irin waɗancan abubuwa da aka ce mace sai ta kiyaye kafin ta kai ga riskar cikar burin ta, shima basu faɗi akan sa ba.
Da farko a matsayin ka na namiji da ke son rayuwar auren sa da matar sa ta yi nasara, to akwai buƙatar ka fara cikawa ko sauke duk haƙƙin da ke wuyan ka da Allah ya ɗora maka na haƙƙin wannan auren (ba zai taɓa yuwuwa ba ka samu nasara a rayuwar auren ka ba alhali haƙƙin da ke kanka kana wasa dashi, hakan shi zai buɗe ƙofar ɓaraka da zata ɓata alaƙar ka da matar ka domin kamar yadda taga baka bata nata haƙƙin ba, kai ma fa kar kayi tsammanin samun naka daga gareta).
Akwai buƙatar bada ingantaccen lokacin ka ga iyalin ka acikin gidan ka, ba wai ka ɗauki iyalin ka cewa basu da lokacin ka da ka ware domin su ba, hakan na nuna basu da wani muhimmanci agare ka, abinda hakan zai haifar maka shine kaima sai su ɗauke ka kamar irin yadda ka ɗauke su ba ka da muhimmanci.
Akwai buƙatar ka zamo babban aboki gareta, ka nuna mata tsantsar SO da ƘAUNA da kulawa, ka girmama ta da irin girmamawan da har sai ta ji cewa bata kai a bata irin wannan girman ba, ka riƙa tunanin ta aran ka, ka zamo mai jin kewar ta a sanda bakwa tare (ka ɗaga waya ka kirata kace kawai ka kira ne don kaji muryar ta saboda kana missing ɗin ta), ka riƙa yin hira da ita, kana mai bata labari mai daɗi, burgewa da ƙayatarwa, ka yi wasa da dariya da ita, kuma ka daraja ta.
Akwai bukatar ka riƙa yaba mata a duk sanda ta kƴautata maka ko tayi wani abu na burgewa domin kai, idan ta durƙushe ka ɗaga ta ka tallafe ta, ka zamo mai yafiya da kauda kai bisa kuskuren ta da ajizancin ta.
Akwai buƙatar ka nuna mata cewa ita ce mutum mafi kusanci da muhimmanci agare ka a duniyar nan musamman da daddare kar ka barta ka tafi can cikin abokai kana hira sai can tsakar dare ka dawo daidai lokacin har tayi barci.
A duk sanda zaka yi ibada don samun kusanci da Ubangiji, ka umarce ta itama ku yi tare, idan kun kammala ku yiwa junan ku da zamantakewar ku addua.
A yayin da ma'aurata s**a iya kiyaye wannan, zamantakewar auren su zai kai ga duk irin nasarar da suke buƙata in sha Allahu.
Alhamdulillah!
Anan na kawo ƙarshen wannan jerin rubutu nawa mai taken NASIHA GA IYAYE MAZA/MATA AKAN AURE.
Ina fatan Allah ya sa waɗanda aka yi domin su, su yi aiki da abinda s**a karanta, ya sanya ya zamo sanadiyyar gyaruwar gidajen auren mu.
Allah ya karɓi abinda yake daidai a ciki, kusakuren ciki kuma ya yafe.
Ina godiya ga ɗaukacin waɗanda s**a bada lokacin su mai tsada s**a bibiyi abinda aka rubuta Ubangiji ya saka musu da alherin sa bisa goyon baya da ƙwarin guiwar da s**a bayar.
Ɗanuwan ku a musulunci Bn-Ahmad Imaam
Nagode.