26/05/2026
RUNDUNAR ‘YAN SANDAN JIHAR BAUCHI
SANARWA GA JAMA’A
BIKIN SALLAH (EID-EL-DUHA 2026): ‘YAN SANDAN BAUCHI SUNA TAYA MUSULMI MURNAR SALLAH, SUN KUMA BA DA SHAWARI DA GARGADI KAN TSARO
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi tana taya dukkan Musulmi a jihar da fadin Nijeriya murnar Sallah Eid-el-Duha da za a yi a ranar Laraba 27 ga Mayu 2026, In ALLAH YA yarda.
Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Sani-Omolori Aliyu, mni, psc(+), ya taya al’ummar Musulmi murnar Sallah, kuma ya yaba da yadda suke taimaka wa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen kiyaye zaman lafiya a jihar.
Domin tabbatar da an yi Sallah lafiya, an tura jami’an tsaro masu yawa zuwa filayen Sallah, manyan hanyoyi, wuraren bukukuwa/wasanni da sauran wuraren jama’a a dukkan kananan hukumomi 20 na jihar. Wadannan jami’an sun hada da ‘yan sanda na yau da kullum, 'yan sandan ko ta kwana da na kwantar da tanzoma, da masu kula da zirga-zirga da kiyaye hadari, suna kuma aiki tare da sauran hukumomin tsaro da ‘yan banga.
Sai dai Kwamishinan ya gargadi duk mai shirin haddasa matsala ko tada zaune tsaye a lokacin shagulgulan Sallar. Ya ce ‘yan ta’adda da masu tayar da hankali su nisanci jihar, domin ‘yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ya karya doka, kamar su ‘yan daba, masu tuƙin ganganci, amfani da not awut (knock out), masu toshe hanyoyin jama'a, da sauran laifuka.
Ya kuma bukaci iyaye da masu kula da yara tare da sa ido kan halayyar ‘ya’yansu domin kada su shiga matsala da za ta kai su hannun shari’a.
‘Yan sanda na rokon hadin kan jama’a ta hanyar bayar da rahoto kan duk wanda ake zargi, ko motsi, ko abu da ake ganin ba daidai ba a ofishin ‘yan sanda mafi kusa, ko kuma a kira lambobin gaggawa: 08151849417,
07031961762,
08050404039.
Kwamishina Omolori ya tabbatar wa al’ummar Bauchi cewa ‘yan sanda za su tabbatar da tsaro kafin, lokacin da bayan hidimomin Sallar. Ya yi addu’ar Allah ya ba kowa albarka, zaman lafiya da kariya.
SP Nafiu Habib, ANIPR, FFIS
Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan Sanda
A madadin: Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi
25 ga Mayu, 2026.