Gololo Youths Movement for development

Gololo Youths Movement for development To foster peace, unity, and cooperation among members.

Assalamu AlaikumYan uwa a yau 17/3/2026 mun gudanar da rabon kayan abinci da turmin zani guda 2 ga kwamitin marayu karka...
17/03/2026

Assalamu Alaikum

Yan uwa a yau 17/3/2026 mun gudanar da rabon kayan abinci da turmin zani guda 2 ga kwamitin marayu karkashin Kungiyar mu ta GOLOLO YOUTHS DEVELOPMENT ASSOCIATION (GYDA) wanda Kungiyar BALA WUNTI SUPPORT ORGANIZATION GAMAWA LG ta bamu. Kwanaki uku da s**a wuce wannan qungiyar ta BWSO ta buqaci mu tura wakilanmu na GYDA Gamawa inda s**a bamu kananan buhun shinkafa guda 8 da kuma Turmin zani guda biyu kamar yadda zaku gani a hoto.

Biyo bayan wannan mun juye wadannan buhunan inda muka rabawa iyayen marayu da gajiyayyu guda 29 kamar yadda sunansu da adireshinsu yake a hoto, don su samu abinda zasu ciyar da iyalansu.

Da wannan muke jaddada godiyar mu ga BWSO Gamawa Local Government Chapter bisa wannan tallafi da s**a bamu don mu amfani al'ummar mu.

26/09/2025

Aikin feshi na maƙabartar Arewa Dake Garin Gololo.. A ƙarkashin wannan kungiya ta mu Mai Albarka ta matasan Garin Gololo.. Allah ya sakawa kowa Da Alkhairi...

Kungiyar matasan garin Gololo

22/09/2025

GOLOLO YOUTH MOVEMENT FOR DEVELOPMENT

Motto: United We Rise

SAKON GAYYATA ZUWA AIKIN GAYYA

Assalamu Alaikum,
Kungiyar matasan Gololo na sanar da za a gudanar da aikin gayya na tsaftace makabartu ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Gololo. Ayyukan da za a yi sun haɗa da:

•Cike guraben kaburbura da dabbobi s**a lalata.

•Yanke ciyawa da share share.

•Feshi da maganin ciyawa.

•Tsabtace wurare gaba ɗaya domin ƙara darajar makabartu.

Lokaci da Wuri:

📌 Juma’a, 26/09/2025 – 9:00 na safe – Makabartar Arewa

📌 Litinin, 29/09/2025 – Zagaye na biyu

Taimako:
Ana roƙon masu hali da su taimaka da kuɗi ko kayan feshi, sauran ’yan uwa kuma su halarta da kayan aiki.

Sako:
Kungiyar Matasan Garin Gololo

Yadda Aikin Gayya na garin Gololo yake tafiya, A inda aka samu halartar mai Girma Sarkin Gololo Da Kanshi. Allah ya saka...
15/09/2025

Yadda Aikin Gayya na garin Gololo yake tafiya, A inda aka samu halartar mai Girma Sarkin Gololo Da Kanshi. Allah ya sakawa kowa da alkhairi.. Tabbass in muka hade kanmu waje Guda Zamu samu irin chanji da mukeso, Fatan mu dai Allah ya Bamu shugabanni Masu Tausayi da kishin Al'uma

Gayyah! Gayyah! Gayyah!. Muna tunasar da yan uwan mu matasa akan aikin gayyah da zamuyi gobe in sha Allah 7-8am Na safe ...
14/09/2025

Gayyah! Gayyah! Gayyah!.

Muna tunasar da yan uwan mu matasa akan aikin gayyah da zamuyi gobe in sha Allah 7-8am Na safe anan bakin kasuwar Gololo.. Allah ya bada ikon Halatta..

11/09/2025

Tabbas Duk lokacin Da Shugaba yayi abun a yaba ya kamata mu yaba masa, Duk da dai Nauyi ne Al'umarsa ya sauke, Amman tabbas Naji Dadin labarin da nake Samu Na Cewa Chairman Na Gamawa wato Hon Madaki Gololo Ya Samar da aiki Na Asibiti A cikin Garin Gololo wannan abun a yaba masa ne Daman irin wadannan Abubuwan ne muke ta kira da Shugabanni su duba, Muna fatan Allah ya basu ikon cika wannan Alkawarin, kuma muna Adduar Duk inda ake da korafi Allah ya basu ikon Dubawa.. Allah yajibanci Lamuranka Yasa A wanye Lafia.

Matasan Gololo masu kishin Gari

To foster peace, unity, and cooperation among members.

08/09/2025

WAKAFA BIL MAUTI WA'IZAN... Allah ya kyautata makwanci kadir

Cikin kaduwa, jimami da kuma alhini Muke sanar da Manbobi Na Wannan kungiya Rashi Na Abokin mu Abdulkadir k mato.. Muna ...
06/09/2025

Cikin kaduwa, jimami da kuma alhini Muke sanar da Manbobi Na Wannan kungiya Rashi Na Abokin mu Abdulkadir k mato.. Muna Adduar Allah yajikan shi, ya yafe mishi yasa mutuwa hutuce a Gareshi, Idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani

Kungiyar Matasan Gololo

Address

Address: No: 10 Bakin Kasuwa Gololo, Gamawa Local Government
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gololo Youths Movement for development posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share