17/06/2026
Da ɗumi-ɗumi: Ƙungiyar (CAND) Ta Nemi A Binciki Sanata Abdulaziz Yari Kan Ɗanyen Zinare Na Naira Biliyan 4.4 Da Hukumar EFCC Ta K**a Ana Ƙoƙarin Fita Da Shi Ƙasar Waje A Jihar Kano
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, (EFCC) ta tsananta bincike kan wani ɗanyen zinare da ta k**a a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, mai nauyin kilogiram 22.2, wanda darajarsa ta kai kusan Naira Biliyan 4.4, da ake zargin ana yunƙurin safarar sa zuwa ƙasar waje ba bisa ƙa'ida ba.
Rahoton shafin (Billionaires.Africa) da aka wallafa a ranar 15 ga Yuni, 2026, ya ce jami'an EFCC na shiyyar Kano sun k**a wani jami'in tsaro na Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA), Anas Baffa, bisa zargin ɓoye ɗanyen zinaren a cikin wandonsa domin tsallake binciken tsaro a filin jirgin kafin a miƙa shi ga wasu fasinjojin da ke shirin tafiya ƙasar waje.
Rahoton ya kuma ce wata ƙungiyar fararen hula mai suna Coalition for Accountability and National Development (CAND) ta yi kira ga hukumomin tsaro su zurfafa bincike kan safarar zinare da haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba, tana mai zargin cewa ya k**ata a binciki wasu manyan mutane kan lamarin, ciki har da Sanata Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan Jihar Zamfara.
A cewar daraktan ƙungiyar, Ibrahim Musa, irin waɗannan ayyuka na jawo asarar kuɗaɗen shiga ga gwamnati tare da ƙara rura wutar matsalolin tsaro a wasu sassan ƙasar.
Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, EFCC ba ta ambaci sunan Sanata Abdulaziz Yari a matsayin wanda ake zargi a hukumance ba dangane da binciken, kuma babu wata sanarwa daga hukumar da ta tabbatar da zarge-zargen da ƙungiyar CAND ɗin ta yi.
A gefe guda kuma, a wani bidiyo da ya wallafa a shafin Tiktok, wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, Junaidu Aminu, ya bayyana cewa ana gudanar da bincike kan wani jirgin kamfanin Ethiopian Airlines a Filin Jirgin Sama na Kano.
Ya yi zargin cewa an gano wasu akwatuna guda 15 da aka ɓoye bayanan abubuwan da ke cikinsu, waɗanda ake zargin suna ɗauke da kayayyaki masu haɗari.
Junaidu, ya kuma yi iƙirarin cewa haƙar ma'adanai ta ɓarauniyar hanya na da alaƙa da matsalolin tsaro k**ar garkuwa da mutane da ayyukan ƴan fashin daji a Arewa, musamman a Jihar Zamfara, yana mai cewa wannan kamun alama ce ta ƙoƙarin hukumomi na daƙile irin waɗannan ayyuka.
Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da wata ƙungiyar fafutuka mai suna "Mai Kare Talakawa" da ke Sokoto ita ma ke tambayar tushen arziƙin Sanata Abdulaziz Yari.
A cewar rahoton Billionaires.Africa, ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda kamfanin Yari, MA'AM Energy Limited, ya sayi kaso mafi rinjaye, kusan kashi 95 cikin ɗari na kamfanin Geregu Power Plc daga hannun attajiri Femi Otedola a watan Disambar 2025, a wata yarjejeniya da aka ƙiyasta cewa darajarta ta kai Naira Tiriliyan 1.08.
Sai dai, babu wata hukuma da ta tabbatar da cewa akwai alaƙa tsakanin wannan harkar kasuwanci da binciken safarar zinaren da EFCC ke gudanarwa. Haka kuma, Sanata Abdulaziz Yari bai fito ya yi martani kai tsaye ga zarge-zargen da wasu ƙungiyoyi da masu sharhi s**a yi ba.