Atta'awun Societal support development foundation

Atta'awun Societal support development foundation this page is for pestering the visibility of Atta'awun activities in and out of Nigeria

02/03/2026

Yan'uwa karmu gajiya da posting da shearing hade da addu'a har sai munga malaminmu ya shaki iskar yanci cikin aminci

Gobe ne zaman kotu 24/2/26 muna fatan daga gobe wahala ya kare Kenan

FREE SHEIKH SANI KHALIFA

18/02/2026

Gina Mai sallah yafi Gina masallaci

18/02/2026
Gidauniyar Atta'awun societal support development foundation karkashin jagorancin Hon. Sadiq sulaiman shu'aibu ta kaddam...
18/02/2026

Gidauniyar Atta'awun societal support development foundation karkashin jagorancin Hon. Sadiq sulaiman shu'aibu ta kaddamar da makarantar karatun Al'qur'ani da darussan islamiyya hadi da kayan karatu da rubutu kyauta a karamar Hukumar Dass.

Kimanin mutum 100 ne zasuci gajiyar karatu kyauta a karamar Hukumar Dass inda a Wannan makaranta duk yaron da ya samu kansa a ciki to zaiyi karatu ne ba tare da biyan ko sisin kobo ba, wannan yunkuri ya samu ne bisa ganin yadda za'abi a dasa wa kananun Yara masu tasowa ilimin addini tare da ingantaccen tarbiyya don ganin an samu Al'umma ta gari abin koyi.

Wannan shiri na karatu kyauta an mishi suna da (Revolution of mindset of under 15 years) wato “sauyin tunanin yara yan ƙasa da shekara 15” da zai gudana karkashin kulawar cibiyar da kuma da Kuma hadin guiwar iyayen Yara kamar yadda aka Saba.

A yayin jawabin Bude makarantar Dr. Kamilu Aliyu Muhammad Bununu yayi Jan hankalin ga iyayen wadannan Yara wajen muhimmancin karatun Addini da na zamani tare da ingantaccen tarbiyya, kana ya ja hankalinsu wajen Kula da wannan makarantar da turo yaran zuwa makaranta sakamakon wannan cibiyar ta dauke nauyin biya wa wadannan Yaran kudin makaranta.

Hakazalika shima shugaban cibiyar Hon. Sadiq ya bayyana maqasudinsa na Bude wannan makaranta inda yace yin hakan Yana cikin aikin wannan cibiyar na bada tallafi da cigaban Al'ummah, ya Kara da cewa burinmu shine mu canzawa wadannan Yara tunanin zaman banza a gari da yawace uawace da tallace tallace da Kuma nunamusu muhimmancin karatun Addini da tarbiyya Sabanin yanda wasu daga cikin matasan namu Suke a yanzu na babu Arabi babu boko Kuma ba Sana'a da zai riqe Wanda zai iya rike rayuwar sa da shi.

MUHAMMAD ALMARKAZY✍️

19/09/2025

ZIYARA DA ATTA-AWUN SOCIETAL SUPPORT DEVELOPMENT FOUNDATION TAKAI A SPECIAL HOSPITAL BAUCHI

Address

12 Reinsurance Hause Ahmad Bello Way
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Atta'awun Societal support development foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share