Orphans Care Committee Jibwis Gwallaga Bauchi

Orphans Care Committee Jibwis Gwallaga Bauchi Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Orphans Care Committee Jibwis Gwallaga Bauchi, Non-Governmental Organization (NGO), Masallacin Juma'ah na Gwallaga, Bauchi.

HUKUMAR BUNƘASA AREWA MASO GABAS (NEDC) TA KAWO TALLAFIN KAYAN ABINCI GA MARAYUA ranar Asabar da ta gabata, Hukumar Bunƙ...
04/06/2026

HUKUMAR BUNƘASA AREWA MASO GABAS (NEDC) TA KAWO TALLAFIN KAYAN ABINCI GA MARAYU

A ranar Asabar da ta gabata, Hukumar Bunƙasa Arewa Maso Gabas (North East Development Commission – NEDC) ta kawo tallafin kayan abinci ga Kwamitin Kula da Marayu na JIBWIS Gwallaga, ƙaramar hukumar Bauchi (Orphans Care Committee).

Kayan tallafin da Hukumar ta kawo sun haɗa da:

Shinkafa (25kg buhu 30)
Man gyada (katan 3)
Sugar Buhu 1

A cikin jawabin da babban jami’in da ya jagoranci kawo tallafin Engineer Sulaiman, ya bayyana cewa Hukumar ta gamsu matuƙa da yadda Kwamitin ya gudanar da rabon tallafin farko da aka bayar a watan Ramadan, inda aka tabbatar da cewa kayan sun isa ga waɗanda s**a cancanta cikin tsari da gaskiya.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Kula da Marayu na JIBWIS Gwallaga Bauchi, Imam Muhammad Ibn Ali, ya mika godiya ta musamman ga Hukumar NEDC bisa wannan ƙarin tallafi da ta kawo a lokaci mai muhimmanci. Ya kuma tabbatar da cewa za a raba kayan cikin adalci, amana da gaskiya, kamar yadda aka yi a baya.

A ƙarshe, muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka wa duk wanda ya bayar da gudunmawa ko ya taimaka wajen ganin wannan tallafi ya iso hannun marayu. Allah Ya saka da alheri, Amin.

JIBWIS Social Media
Bauchi LGA

KWAMITIN KULA DA MARAYU TA TALLAFA WA MARAYU KIMANIN 1,300 DA NAMAN LAHIYAA ranar Asabar, 30/05/2026, Kwamitin Kula da M...
04/06/2026

KWAMITIN KULA DA MARAYU TA TALLAFA WA MARAYU KIMANIN 1,300 DA NAMAN LAHIYA

A ranar Asabar, 30/05/2026, Kwamitin Kula da Marayu na JIBWIS Gwallaga, Ƙaramar Hukumar Bauchi (Orphans Care Committee), ta gudanar da rabon naman lahiya ga gidajen marayu 265.

A cikin jawabinsa, Shugaban Kwamitin Kula da Marayu, Imam Muhammad Ibn Ali, ya bayyana cewa tun farko kwamitin ta yi niyyar tallafa wa marayu 10,000 da naman lahiya a wannan Shekaran.

Sai dai saboda ƙarancin dabbobin da aka samu, an canza tsarin rabon zuwa gida-gida domin marayu da dama su samu su amfana.

Haka kuma, shugaban ya yi kira ga mawadata, 'yan siyasa da sauran masu hannu da shuni da su ji tsoron Allah, su ci gaba da tallafawa irin waɗannan kwamitoci da ke kula da rayuwar marayu, tarbiyyarsu da walwalarsu.

A nasa jawabin, Sakataren Kwamitin, Malam Usamatu Lawan Muhammad yace saboda ƙarancin dabbobin layya da aka samu, sai aka zaɓi gidaje 265 da ke da marayu domin su amfana da tallafin, inda aƙalla kowane gida ke da marayu biyar da s**a ci gajiyar rabon.

A ƙarshe, kwamitin ta miƙa godiya ta musamman ga waɗanda s**a bayar da gudummawa domin nasarar wannan aiki na alkhairi:

1. Haj. A'ishatu Bala Abdulkadir Muhammad (Matar Maigirma Gwamnan Jihar Bauchi, Uwar Marayun Bauchi)
2. Alh. Garba Muhammad Noma/Jarman Bauchi ( Ta hanun Alh. Sirajo Jibrin)
3. Al-Muhsin Foundation Tilden Fulani, Toro Local Government Bauchi State Nigeria
4. Prof. Mansur Isa Yelwa
5. Imam Dr. Abdurrahman Ibrahim Idris
6. Dr. Babayo Yakubu Adamu
7. Masallatan rassan Kwamiti

Haka zalika, kwamitin ta gabatar da nasihohi masu jan hankali ga marayun, tare da ƙarfafa musu gwiwa kan neman ilimi, kyawawan ɗabi'u da tsoron Allah, domin su zama mutanen kirki waɗanda addinin Musulunci da al'umma za su yi alfahari da su a nan gaba.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka wa dukkan masu hannu a wannan aikin alkhairi da mafificin alheri, Ya karɓi ibadunsu, Ya albarkaci dukiyoyinsu, kuma Ya saka musu da Aljannatul Firdausi.

JIBWIS Social Media

AN TUFATAR DA MARAYU 5,011 DA KAYAN SALLAH A KARAMAR HUKUMAR BAUCHI.A ƙoƙarinta na inganta rayuwar marayu da kuma kyauta...
26/03/2026

AN TUFATAR DA MARAYU 5,011 DA KAYAN SALLAH A KARAMAR HUKUMAR BAUCHI.

A ƙoƙarinta na inganta rayuwar marayu da kuma kyautata tarbiyyarsu, Kwamitin Kula da Marayu na JIBWIS Gwallaga, Karamar Hukumar Bauchi, ta tufatar da marayu guda 5,011 a faɗin ƙaramar hukumar.

Kamar yadda kwamitin ta saba gudanar da irin wannan aiki na alkhairi, an gudanar da rabon kayan a ranar Asabar, 25 ga Ramadan 1447H (14 ga Maris, 2026).

Haka zalika, an gabatar da NASIHOHI masu ratsa jiki ga marayun da iyayen riƙonsu, domin su zama mutanen kirki waɗanda al’umma za su yi alfahari da su a nan gaba.

Domin sauƙaƙa gudanar da aikin, kwamitin ta samar da rassa guda 18. Daga ciki, rassa 13 na cikin gari sun haɗu a Masallacin Gwallaga, inda aka raba su zuwa cibiyoyi shida domin inganta tsarin rabon kayan.

Haka kuma, kwamitin ta kai kayan zuwa rassa guda 5 na wajen gari, domin rage wahalar zirga-zirga da sauƙaƙa wa jama’a karɓar tallafin.

A cikin jawabinsa, Shugaban Kwamitin Kula da Marayu na JIBWIS Gwallaga, Imam Muhammad Ibn Ali, ya kara jan kunnen marayun so zamo nagari, suke zuwa Makaranta da kulawa da ibada.

Ya kuma miƙa godiyarsa ga masu hannu da shuni da s**a bayar da gudunmawa wajen gudanar da wannan aiki na alkhairi.
Daga cikinsu akwai:

1. Sen. Shehu Buba Umar

2. Haj. Aisha Bala Abdulkadir Muhammad (Uwar Gidan Gwamnan Jihar Bauchi kuma Uwar Marayun Bauchi)

3. Alh. Rabiu Barau

4. Alh. Umar Barau Ningi

5. Sen. Abubakar Maikafi (Danmadamin Bauchi)

6. Alh. Abdu Hassan (Sarkin Sudan Bauchi)

7. Hon. Alh. Adamu Usman Sufi

8. Haj. Aisha Old GRA, Bauchi

9. Garu Islamic Health Technology Bauchi

10. NEDC Bauchi

Da sauransu.

Har ila yau, ya ƙara kira ga masu hali da su ƙara taimakawa, musamman ganin rabon naman layya da ke tafe.

A ƙarshe, muna roƙon Allah Ya saka wa dukkan waɗanda s**a taimaka da alheri, Ya kuma ƙara musu arziki mai albarka. Ya hadamu da Manzon Allah (SAW) cikin Aljannar Firdausi.

JIBWIS Social Media
Bauchi LGA

24/03/2026

Address

Masallacin Juma'ah Na Gwallaga
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Orphans Care Committee Jibwis Gwallaga Bauchi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share