20/12/2024
Godiya ta Musamman bisa ga amsa Roƙonmu da Ci gaba da Tallafawa sabida Jin dadin Al'uma,
A madadin Yan uwa Mazauna wannan yanki.
Mai girma dan majalisar Jiha, Funakaye ta arewa.
Muna mika godiyarmu ga gaggawar amsawa da kuma jajircewarku wajen samar da mafita dangane da gyaran transformer Unguwar KORAGO/SANGRU a Bajoga. Yunkurin da kuka yi na magance bukatun al’umma hakika abin a yaba ne, kuma muna godiya da kokarinku.
Muna kuma mika godiyar mu ga shugaban karamar hukumar Funakaye da ya samu halartan aikin gyaran na’urar taransfoma. kuma muna godiya da jagorancin ku.
A yayin da muke ci gaba da hada kai don inganta al’ummarmu, har wa yau muna so ku Kara jajircewa akan jajircewar ku domin kawo mana dauki kan matsalar rashin ruwan sha. Mazauna Unguwar tamu ta KORAGO na fama da matalar lokaci Mai tsawo, Muna neman taimakon ku don magance wannan lamari cikin gaggawa.
Ina sake gode muku bisa goyon baya da jajircewarku ga jin dadin al'ummarmu.
Muna godiya Matuka.
Allah Ya Albarkaci Bajoga, Funakaye, Gombe da Najeriya baki daya.