23/03/2026
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh
Alhamdulillah. Muna mika godiya ta musamman ga dukkanin waɗanda s**a bada gudummawa wajen wannan aikin alkhairi na rabon abinci a cikin kwanaki 10 na ƙarshe na Ramadan.
Da yardar Allah, an samu nasarar:
– Rabon buhunan masara 5 ga gidaje 160
– Rabon Cartons 12 na spaghetti ga gidaje 40
– Rabon buhunan ruwa 200 a cikin kwanaki 10
Wannan aiki ba zai yiwu ba sai da goyon bayan ku. Allah Ya saka muku da alkhairi, Ya karɓi sadakarku, Ya sanya shi a cikin ma’aunin ayyukanku na alheri.
Allah Madaukakin Sarki Yace:
"Misalin waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu a tafarkin Allah kamar ƙwayar hatsi ne da ta tsiro ta bada zangarniya bakwai, a kowace zangarniya akwai hatsi ɗari..." (Suratul Baqarah 2:261)
Manzon Allah (SAW) ya ce:
"Sadaka ba ta rage dukiya." (Muslim)
Muna kira ga kowa da kowa da ya ci gaba da tallafawa irin waɗannan ayyuka na jin ƙai da taimakon al’umma. Ko da kaɗan ne, yana da daraja a wurin Allah.
Jazakumullahu Khairan. May Allah reward every contributor abundantly.