Kofar Gabas Community Forum

Kofar Gabas Community Forum Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kofar Gabas Community Forum, Community Service, Kofar Gabas, Azare.

A cikin kokarin wannan zaure namu mai albarka, mun rabawa kimanin yara 30 littafan rubutu, kowannen su ya samu littafai ...
28/09/2025

A cikin kokarin wannan zaure namu mai albarka, mun rabawa kimanin yara 30 littafan rubutu, kowannen su ya samu littafai 3 don taimakawa wajen huɓɓasa ilimi a fadin unguwar.

28th September, 2025.

yau wannan ƙungiya tamu mai albarka ta fara gudanar da dubiya da kuma bada magani ga masu cutar zazzaɓin cizon sauron, t...
14/09/2025

yau wannan ƙungiya tamu mai albarka ta fara gudanar da dubiya da kuma bada magani ga masu cutar zazzaɓin cizon sauron, tare da basu magani kyauta.

Wannan ƙuduri za'a gabatar da shi ne, ma kimanin yara 60 masu shekaru daga 12 zuwa ƙasa. Kuma gabatar dashi a cikin kwanaki 3.

Allah ya saka mana a mizani.

A cikin kokarinmu na bada gudunmawa wajen yaki da zazzabin maleriya, wannan kungiya tana gayyatar yara masu shekaru ƙasa...
13/09/2025

A cikin kokarinmu na bada gudunmawa wajen yaki da zazzabin maleriya, wannan kungiya tana gayyatar yara masu shekaru ƙasa da 10 har guda 60, domin yi musu maganin maleriya kyauta.

kamar yadda sabon zangon karatu ya fara, wannan zaure namu mai albarka ya biya kudin makaranta na ɗaliban da muka saka a...
13/09/2025

kamar yadda sabon zangon karatu ya fara, wannan zaure namu mai albarka ya biya kudin makaranta na ɗaliban da muka saka a islamiyya.

Da fatan Allah ya kara bamu damar ci gaba da irin waɗannan ayyuka na alkhairi.

Daga cikin ayyukan wannan zaure ta bangaren ilimi, an samu nasarar saka yara biyu a islamiyya, an biya musu kudin regist...
08/04/2025

Daga cikin ayyukan wannan zaure ta bangaren ilimi, an samu nasarar saka yara biyu a islamiyya, an biya musu kudin registration, ɗinkin uniform da kuma biyan kudin makaranta.

Wannan aiki an gudanar da shi ranar 11 January, 2025.

Daga cikin ayyukan wannan zaure, mun samar da kayuwan fanfo, don maganin zubar da ruwa, da kuma inganta muhalli.An gabat...
07/04/2025

Daga cikin ayyukan wannan zaure, mun samar da kayuwan fanfo, don maganin zubar da ruwa, da kuma inganta muhalli.

An gabatar wannan aiki ranar 4 April, 2025.

07/04/2025

DALILAN BUDE WANNAN ZAURE, DA KUMA AYYUKAN DA YA TUNKARA.

An ƙirƙiri Wannan zaure ranar 1 January, 2025 don gudanar da muhimman abubuwa kamar haka:

1. Cigaban Ilimi a tsakanin mazauna yankin.

2. Samar da hanyoyin koyar da sana'a a tsakanin matasa.

3. Tsaftace muhalli da inganta ayyukan da s**a shafi lafiya.

4. Ayyukan cigaban al'umma, da kuma

5. Samar da tsaro.

Wadannan manufofi (objectives ) sune duga-dugan da ƙungiyar ke zaune a kansu, kuma an gina su akan kyakkyawar manufa, da zummar haɗa kan dukkan mazauna yankin ba tare da banbancin shekaru, jinsi ko akida ( ta siyasa ko ta addini) ba.

Allah ya taimaki wannan ƙuduri, ya dauwamar da shi, ya sa kuma ya amfani al'umma.

Yau Litinin 7 April, 2025. Wannan zaure namu mai albarka ya shirya horaswa ga dalibai masu rubuta jarabawar JAMB kuma ya...
07/04/2025

Yau Litinin 7 April, 2025. Wannan zaure namu mai albarka ya shirya horaswa ga dalibai masu rubuta jarabawar JAMB kuma yan asalin Kofar Gabas.

1. An samu nasarar basu shawarwari da kuma nusar da su muhimmancin abunda suke tunkara.

2. Sannan za'a shirya musu bita, ta yadda za'a gwada musu yadda zasuyi amfani da computer wajen rubuta jarabawar.

3. Za kuma a shirya bita, na wasu muhimman darussa ga dalibai don tunkarar wannan jarabawa.

Muna fatan Allah ya cigaba da taimakon wannan hubbasawa da samarin unguwar suke sa a gaba.

Address

Kofar Gabas
Azare

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kofar Gabas Community Forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share