Sameer Salihu Charity Foundation

Sameer Salihu Charity Foundation Empowering women and Youth

Sameer Salihu Charity Foundation
18/08/2026

Sameer Salihu Charity Foundation

’Yan Sanda Sun Tone Wani Abubuwan Fashewa a Wani Babban Titin ZamfaraRundunar ’Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Zamfara ...
18/08/2026

’Yan Sanda Sun Tone Wani Abubuwan Fashewa a Wani Babban Titin Zamfara

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Zamfara ta yi nasarar gano tare da tone wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan bindiga ne s**a dasa a babban titin Kaura Namoda zuwa Moriki.

Rundunar ta ce an ɗauki matakan da s**a dace domin tabbatar da tsaron hanyar da kuma kare rayukan matafiya.

17/08/2026

Yau anyima fanarabul korar kare😅😆😁
17/08/2026

Yau anyima fanarabul korar kare😅😆😁

17/08/2026

Koko To Zuru Road Reaching 98% Completion.

’Yan Sanda Sun K**a Wani Mutum Kan Zargin Binne Al-Qur’ani da Abubuwan Tsafi a ZuruRundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta k...
15/08/2026

’Yan Sanda Sun K**a Wani Mutum Kan Zargin Binne Al-Qur’ani da Abubuwan Tsafi a Zuru

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta k**a wani mutum mai suna Abubakar Musa, mai shekaru 29, mazaunin ƙauyen Rafin Mose da ke ƙaramar hukumar Zuru, bisa zargin haɗa baki, tozarta littafin addini, amfani da tsafi da sihiri, da kuma tayar da zaune tsaye.

Kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 9 ga Agustan 2026, da misalin ƙarfe 7:00 na yamma, a yankin Zango da ke Zuru.

A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya haɗa baki da wasu mutane biyu, Rabi’u Tela, mijin Zarau Hassan, da Hamza Zango, waɗanda s**a tsere, inda ake zargin sun haƙa rami a cikin ɗakin Zarau Hassan tare da binne Al-Qur’ani da wasu abubuwa.

’Yan sandan sun ce daga cikin abubuwan da aka binne tare da Al-Qur’ani akwai maniyyi, goro fari da ja, kayan ciki, matattun dabbobi da wasu abubuwan da ake zargin na tsafi ne.

Rundunar ta ce ana zargin an aikata hakan ne da nufin sanya Zarau Hassan ta kasance mai biyayya ga mijinta, Rabi’u Tela, abin da ta ce ka iya haifar da rikici da tada hankalin al’ummar Musulmi.

A halin yanzu, Abubakar Musa yana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da kokarin cafke Rabi’u Tela da Hamza Zango.

Rundunar ta bayyana cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, CP Umar M. Hadejia, ya yi Allah-wadai da lamarin, tare da jaddada cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da laifin da ka iya barazana ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Kwalejin Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Dakingari na samun ci gaba a ƙarƙashin Gwamna Idris – Shugaban KwalejinShugaban Kwa...
15/08/2026

Kwalejin Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Dakingari na samun ci gaba a ƙarƙashin Gwamna Idris – Shugaban Kwalejin

Shugaban Kwalejin Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Dakingari, Dakta Abubakar Boyi Dalatu, ya ce makarantar na samun ci gaba a hankali a ƙarƙashin goyon baya da tallafin Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris, Kauran Gwandu.

Dakatar Dalatu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a harabar wucin-gadin kwalejin da ke Dakingari.

Taron ya samu halartar Kwamishinan Ilimi Mai zurfi na jihar, Abubakar Isah Tunga, da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi.

Shugaban kwalejin ya ce goyon baya da ƙarfafa gwiwar da gwamnatin jihar ke bai wa makarantar ya taimaka wajen farfaɗo da harkokin karatu, tare da ƙara yawan ɗaliban da ke samun guraben karatu a kwalejin.

Ya tunatar da cewa an kafa Kwalejin Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Dakingari shekaru 14 da s**a gabata, da nufin samar da ingantaccen ilimin fasaha ga al’ummar jihar.

Dakta Dalatu ya ƙara da cewa a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Nasir Idris, kwalejin ta faɗaɗa shirye-shiryen koyar da fasaha, musamman a fannonin sabbin fasahohi masu tasowa.

Ya ce hakan na daga cikin ƙoƙarin bai wa ɗalibai ƙwarewar fasaha da za ta taimaka musu wajen taka muhimmiyar rawa a ci gaban tattalin arziki da zamantakewar Jihar Kebbi da ƙasa baki ɗaya.

Jagorah
15/08/2026

Jagorah

Address

Argungu

Telephone

+2349133426263

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sameer Salihu Charity Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Sameer Salihu Charity Foundation:

Shortcuts

Share