30/08/2026
ππππππππ ππππππππππππ π
πππππππππ
GIDAUNIYAR VELOCITY HUMANITARIAN FOUNDATION TA ΖARA TALLAFA WA FATIMA ADAMU DAGA MALAM INA BAYAN ΖAUKAR NAUYIN JINYARTA.
Gidauniyar Velocity Humanitarian Foundation (VHF) ta Ζara tallafa wa Fatima Adamu, mai shekaru 8, mazauniyar Malam Ina, bayan da gidauniyar ta Ιauki nauyin jinyarta.
A wannan karon, gidauniyar ta kashe jimillar Naira Dubu Dari Hudu da Ashirin (β¦420,000) wajen tallafa wa iyalanta da kayan abinci, kuΙin cefane da sauran abubuwan da suke buΖata wajen kula da jinyarta.
Wannan tallafi ya sake tabbatar da jajircewar gidauniyar wajen tsayawa tare da marasa lafiya da iyalansu, musamman waΙanda ke fuskantar Ζalubalen rashin wadatattun kuΙaΙen kula da jinya da bukatun yau da kullum.
Gidauniyar na ci gaba da tsayawa kan manufarta ta ceto rayuka, rage wa iyalai radadin wahalar jinya, da tallafa wa masu buΖata domin samun damar gudanar da rayuwa cikin sauΖi da kwanciyar hankali.
30, August 2026.
Khaleed Shehu Kaabo
Assistant Secretary
Velocity Humanitarian Foundation