ELTAF News TV

ELTAF News TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from ELTAF News TV, Area 10, Abuja.

Majalisar Malamai a Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da ganin jinjirin watan shawwal a yankunan da dama na kasar da s**a haɗ...
18/03/2026

Majalisar Malamai a Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da ganin jinjirin watan shawwal a yankunan da dama na kasar da s**a haɗa da Diffa da Zinder,

Don haka gobe Alhamis ce ranar Sallah ƙarama a faɗin ƙasar.

09/03/2026

Happy blessed month of Ramadan ELTAF News TV

FASSARAR WASIƘAR AMINU HALLIRU ZAUWA HARSHEN HAUSA: BUƊELADIYAR  WASIƘA ZUWA GA HON. MEMBA (Hon. Abdulkarim Kero)Mai Gir...
08/03/2026

FASSARAR WASIƘAR AMINU HALLIRU ZAUWA HARSHEN HAUSA:

BUƊELADIYAR WASIƘA ZUWA GA HON. MEMBA (Hon. Abdulkarim Kero)

Mai Girma, Ranka Ya Dade,

Na rubuta wannan wasiƙa ne a madadin dimbin matasa da mazauna Mazabar Kaduna ta Kudu, waɗanda ke nuna damuwa da takaici game da irin wakilcin da kuke yi musu a halin yanzu a Majalisar Tarayya.

A yau, wakilan jama’a a Majalisar Wakilai ta Tarayyar Najeriya suna ƙoƙari matuƙa wajen tallafa wa al’ummomin da suke wakilta ta hanyar samar musu da damammaki masu ma’ana. Wasu na nemo guraben aikin gwamnati a matakin tarayya, suna taimaka wa matasa samun aiki a hukumomin gwamnati, suna jawo shirye-shiryen horo, tallafin karatu, da shirye-shiryen ƙarfafa rayuwar jama’a.

Sai dai abin takaici, halin da ake ciki a Kaduna ta Kudu, ya sha ban-ban da irin na wasu yankun.

Yayin da takwarorinku a sassa daban-daban na ƙasar nan ke taimaka wa al’ummominsu wajen samun aikin gwamnati da damammakin aiki masu ɗorewa, wasu daga cikin matasan Kaduna ta Kudu ana ba su ƙananan kuɗaɗe na naira dubu biyar (₦5,000) kacal a wasu lokuta. Da dukkan girmamawa, wannan ba ƙarfafawa ba ne; hanya ce da ke jefa mutane cikin dogaro da taimakon wucin gadi.

Matasanmu sun yi karatu, suna da ƙwarewa, kuma suna da sha’awar yin aiki. Abin da suke buƙata shi ne wakilci wanda zai yi fafutuka domin a haɗa su cikin damammakin da gwamnatin tarayya ke bayarwa, ba wai rabon ƙananan kuɗaɗe da ba su ma iya biyan bukatun yau da kullum ba.

Al’ummar Kaduna ta Kudu ba su zaɓi a ba su tarkace ba. Sun zaɓi a wakilce su, a kare muradunsu, kuma a kawo ci gaba gare su. Sun zaɓi wanda zai buɗe musu ƙofofin damammakin da ke akwai a matakin gwamnatin Tarayya.

Muna sa ran wakilinmu zai yi gwagwarmaya domin samar wa ‘ya’yan mazabar guraben aiki a ma’aikatun tarayya, hukumomi, da sauran cibiyoyin gwamnati. Muna son ƙarfafawa ta hanyar kasuwanci, koyon sana’o’i, da bunƙasa ilimi, domin waɗannan su ne ababen da ke kawo ingantacciyar ƙarfafawa.

Gaskiya ne, raba ₦5,000 ga matasa masu fama da wahalhalu na iya zama kamar karamci, amma ba zai iya magance matsalolin rashin aikin yi, talauci, da jin an ware matasa a wannan mazaba ba.

Mai girma Hon. Memba, shugabanci a yau ba wai game da busa ƙaho ko sanya hula ba ne. Shugabanci yana nufin samun hangen nesa, ƙarfafa gwiwar jama’a, da yin fafutuka domin ci gaban mutanen da kake wakilta.

Kaduna ta Kudu ta cancanci fiye da haka. Matasanmu suna buƙatar damammaki, ba rabon ƙaramin taimako na wucin gadi ba. Don haka wannan wasiƙa kira ne na a sauya salon da zai fifita ƙarfafawa mai ɗorewa, damammaki na gaskiya, da ingantaccen wakilci ga al’ummar da s**a ba ku amanar wakilcin su.

Tarihi zai yi muku hukunci ba bisa yawan kuɗin da kuka raba ba, sai dai bisa damammakin da kuka samar wa al’ummarku.

Matasan Kaduna ta Kudu na kallonku, kuma suna fatan za a ji muryarsu.

Rubutawa: Aminu HALLIRU
Fassara: ELTAF News TV
08:03:2026

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta sanar da haramta ɗaukar hotunan marasa ƙarfi da ake taimakawa da kayan abinci lokacin azum...
19/02/2026

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta sanar da haramta ɗaukar hotunan marasa ƙarfi da ake taimakawa da kayan abinci lokacin azumin Ramadan tare da watsa su a kafafen sada zumunta.

Karin bayani: https://rfi.my/CSUD

19/02/2026

SANARWA: SHIRIN CIYARWA DA RABON KAYAN SALLAH

A karkashin gidauniyar Eltaf Foundation, muna farin cikin sanar da al’umma cewa zamu gudanar da shirin ciyarwa da rabon kayan Sallah ga marasa galihu, marayu, da masu ƙaramin ƙarfi a wannan watan mai alfarma na Ramadan.

Manufar wannan shiri ita ce rage radadin rayuwa ga masu buƙata, da kuma ba su damar gudanar da azumi da shagalin Sallah cikin walwala da farin ciki.

Saboda haka, muna kira ga daukacin al’umma, masu hannu da shuni, da duk masu son aikata alheri da su bada gudunmawar su domin tallafawa wannan shiri mai albarka. Duk gudunmawar da aka bayar, babba ko karama, zata taimaka wajen faranta ran masu buƙata.
Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa duk wanda ya bada gudunmawa da alheri, ya kuma sanya wannan aiki cikin mizanan ayyukan alheri a ranar lahira.

Eltaf Foundation
Domin tallafawa shirin, a tuntubi lambobin da ke jikin sanarwar.

27/01/2026

Gidauniyan ELTAF FOUNDATION ta tallafawa wata baiwar Allah da Bunar Gawayi dun tayi sana'a tare da Jari dan Dogoro da Kai.

RABON TALLAFIN KAYAN AZUMICikin hukuncin Ubangiji da amincewarsa a wannan Shakara 2026  ƙungiyar (ELTAF FOUNDATION) tare...
21/01/2026

RABON TALLAFIN KAYAN AZUMI

Cikin hukuncin Ubangiji da amincewarsa a wannan Shakara 2026 ƙungiyar (ELTAF FOUNDATION) tare da Hadin guiwan ELTAF News TV zamu ziyarci asibi da gidan marayu domin tallafa musu da kayan azumi. Duba da yanayin da ake fama dashi, zamuyi wannan rabon domin rage raɗaɗi. Sannan akwai kayan sallah da zamu ɗinkawa domin rabawa almajirai da masu ƙaramin ƙarfi, Domin kwalliyar Sallah. Muna fatan Ubangiji Allah ya ƙarbi Ibadinmu ya sakawa Jagoran mu Ahmad Yacoubou Ibrahim da Alkairi.

Allah ya cika masa burinsa na alkhairi.

21/01/2026

Alhamdullah

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.Allah ya yi wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa, ɗaya daga cikin fitattun malamai m...
27/11/2025

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.

Allah ya yi wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa, ɗaya daga cikin fitattun malamai masu ilimi, basira da tasiri a fadin Najeriya. Marigayi Sheikh Dahiru ya shahara wajen yada ilimin addini, gyaran tarbiyya, da jan hankalin al’umma zuwa ga zaman lafiya, adalci da tsoron Allah.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kasance jagora mai gaskiya, malami wanda kalamansa ke cike da nasiha da tausayi, tare da bin tafarkin Annabi (SAW) wajen isar da sakon addini. Ya rayu da sadaukarwa wajen gina al’umma da ilmantar da daruruwan dalibai da s**a yada iliminsa a sassan duniya daban-daban.

Allah Ya gafarta masa, Ya yi masa rahama, Ya sanya kabarinsa cikin lambunan Aljanna. Allah Ya ba iyalansa, almajiransa, mabiyansa, da dukkan al’ummar Musulmi hakurin jure wannan babban rashi. Amin.

ELTAF News TV

A jiya kungiyar Eltaf foundation da take nan kasar Niger a capital Niamey, tayi rabon abinci da yakai mutum dari biyar t...
04/10/2025

A jiya kungiyar Eltaf foundation da take nan kasar Niger a capital Niamey, tayi rabon abinci da yakai mutum dari biyar tare da ruwa manyan sachets 200 a babban asibitin gwamnati dayake anna kasar Niger

Address

Area 10
Abuja
80028

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ELTAF News TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to ELTAF News TV:

Share