24/06/2025
ƘALUBALEN GWAGWARMAYA.
(Rubutun yana da ɗan tsawo).
Kamar shekaru takwas baya wajen 2017 mun fara wani movement na ƙungiyarmu mai suna BIRNIWA YOUTH INITIATIVE, wacce muka ayyana a matsayin ƙungiyar da za ta yaƙi matsalolin da muke fama da su k**ar ɓangaren ILIMI, LAFIYA, RUWAN SHA, WUTAR LANTARKI, SUFURI (TRANSPORTATION), TATTALIN ARZIKI da dai sauran abubuwa mak**antan haka. Bakin gwargwado mun cim ma nasara a abubuwa da yawan gaske, wanda mu kanmu ba mu taɓa ma zaton za mu iya cim ma su ba a cikin ƙaramin lokaci haka. Musamman bisa la'akari da ƙananun shekarunmu dan a lokacin idan ba iyayen ƙungiya ba to ba na jin akwai wanda ya kai shekaru 30 a kaf cikinmu, ƴaƴan ƙungiyar.
Daga baya bayan tafiya ta yi nisa, bayan mun yi abubuwa da yawa mun samu haske da ƙarin fahimtar cewa a waɗannan shekarun, kuma a wancan lokacin wanda duk mu da muke gaba gaba a cikin tafiyar gaskiya wannan ba shi ne abin da ya k**ata mu saka a gaba a rayuwarmu ba, duk da cewa abu ne mai kyau a ce ka samar da wata hanya da take warware wasu daga cikin matsalolin al'umma. Iya sanya albarkar mutane da kuma fatan alkairin da za a maka a yayin da ka samar da wani abu na ci gaba guda ɗaya ya fi ƙalubale goma da za ka fuskanta a yayin ƙoƙarin samar da wannan ci gaban. Amma komai lokaci ne da shi.
Daga cikin abubuwan da muka lissafa za mu kawo ci gaba a cikinsu babu wani fanni da ba mu samar da abu ko da guda ɗaya ba ne domin al'umma, wani fannin ma abubuwa da yawa sama da guda ɗaya.
Amma a wancan lokacin kusan dukkan mu babu wanda yake da wani babban kwalin karatu ko wata ƙwaƙƙwarar sana'a ko wani aikin da za a ce shi ne madogararmu basu fi mutum biyu ba da za a iya cewa suna da sana'a tak**ammiya, duk da cewa wasunmu a lokacin sun yi Diploma wasu NCE wasu kuma suna kan yi, idan zan tuna mutum biyu zuwa uku ne kawai suke cikin karatun Degree a wancan lokacin. Dan haka duk abubuwan da muke yi ko muka samar kawai mu namu shi ne kai koken ko ƙorafin zuwa inda muke ganin ya dace da sunan Ƙungiya, sai kuma bibiya da tuni akan abin har zuwa sanda Allah zai sa a samu abin ya kammala ko a yi shi. Amma ba mu da kuɗin da za mu iya kashe da yawa daga cikin matsalolin, tunda yawanci manya ne. Sai daga baya da ake samun ƙananun matsalolin yau da gobe wasu muna iya magance su da ɗan abin da muke samu na buga bugar da muke. Sai muka lura cewa ai muna aiki ne ga wasu amma muna barin kanmu alhalin mu ma ɗin muna buƙatar hakan a rayuwarmu.
Mun nema wa da yawa hanya sun samu ADMISSION a makaranta har a jami'a k**ar ABU, mun nema wa wasu tallafin kuɗin REGISTRATION, mun yi fafutukar da wasu s**a samu AIKI a matakin STATE GOVERNMENT da kuma FEDERAL GOVERNMENT sama da mutum GOMA. Mun nemo SOMO an kafa a wasu wurare, mun MAIDA YARA da yawa zuwa MAKARANTA (primary da secondary), mun yi sanadin zuwan KEDCO har cikin garin Birniwa aka yi taro k**ar dai taron Gwamnati da al'umma a ɗakin taro na Sakateriya, wanda sanadin wannan taron Birniwa ta kusan shekara tana samun wuta yanda ya k**ata kafin a dawo gidan jiya, mun nema wa mutane da yawa TALLAFIN JARI (musamman matan da muka lura suna cikin yanayin buƙatar yin sana'a), mun tura neman GININ T**I wanda ya kai 20KM kuma har ofishin Gwamna takardar ta je an karɓe ta, mun nemi aikin DAM NA RUWA KO YASAR HANYAR RUWA wanda ya tashi daga mazaɓar Matamu ya gangara har Diginsa har zuwa wani yanki na ƙaramar hukumar Maigatari, mun tura takardar ƙorafi a madadin al'umma akan batun gonakin KAMFANIN TUMATIR kuma aka dakatar da yunƙurin karɓar amfanin gona daga hannun Manoma, mun zauna da manyan mutane akan abubuwa da yawa duk dan samun ilimin ciyar da al'umma gaba. Gaskiya mun yi abubuwa da yawan gaske.
A lokacin fa duk mu ma muna buƙatar ƙarin KARATUN, muna buƙatar AIKIN a iya matakin karatun da muka yi idan har damar hakan ta samu, muna buƙatar JARIN idan za a ba mu. Amma k**ar ba mu damu da tamu rayuwar ba, duk da nasara da muke samu amma ba irin zagin da ba mu sha ba, daga makusanta har na nesa. Wanda wasu duk rashin fahimtar me muke yi ne ya sa hakan. Da yawa ba sa iya ganin alkairin da muke shimfiɗawa, ko da suna ganin abin a zahiri amma suna ganin k**ar mun yi kaɗan a ce muna da wannan tunanin, ana ganin mu ba kowa ba ne ba kuma 'ya'yan kowa ba ne, ba mu kai mu yi duk irin wannan ba.
Daga ƙarshe da kanmu muka gane cewa yanzu a wannan matakin namu ba wai GINA AL'UMMA ne damuwar da ya k**ata mu saka a gaba ba, a'a mu fara ƙoƙarin ganin mun GINA KANMU (personal development). Mu tafi mu ƙaro karatu, mu shiga koyon sana'o'i, mu je mu nemi ayyuka, mu yi fafutuka domin mu TSAYA DA ƘAFAFUNMU. Domin tabbas a yanda alamu s**a nuna idan ba mu gina kanmu ba to za a wayi gari ba mu isa mu yi abin da muke ganin muna yi yanzu ba, ba mu isa mu iya zuwa wani wajen a kalle mu ba. Babu karatu mai zurfi, babu sana'a tak**ammiya, babu wani aiki na kamfani ko na gwamnati, da me za mu iya ci gaba da gwagwarmaya? Wanda yake taimako a yi abu shi ma yau da gobe zai sa ya kasa ko kuma ya ji ya gaji, rayuwa ce kowa da irin matsalolinsa.
Wannan ya sa muka ja da baya, muka ajiye abubuwa da yawa sai ɗan abin da ba za a rasa ba lokaci bayan lokaci. Mun lura cewa, har sai zuwa lokacin da za mu iya kallon kanmu a matsayin wasu tsayayyu akan ƙafafunsu sannan ne za mu iya cewa mun kai mu yi duk irin waɗancan abubuwan da sunan gwagwarmaya. Gwagwarmaya idan ba a tsaya da ƙafa ba to sunanta GWARAMA. Komai yana da lokaci mafi dacewa a yi shi. Duk sanda aka fara wani abu akan lokacin da ba nashi ba to ko da an yi shi za a sha matuƙar wahala.
Mun koyi darasi da yawa a waɗannan shekarun gwagwarmayar, amma daga cikin abubuwan da s**a fi tsaya mana a rai kuma s**a fi fahimtar da mu rayuwa akwai abu guda biyu zuwa uku.
Na farko shi ne, duk yanda mutum ya kai da ƙoƙarinsa a kanka, matuƙar ka ci gaba da takura shi akan koma miye to za ka iya gajiyar da shi. Kuma zai iya janye jiki daga gare ka, ko da kuwa yana sane da cewa ba dan kanka kake takura shi ɗin ba, dan al'umma ne. Ɗan Adam duk gajiyayye ne komai daren daɗewa, a yi yau a yi gobe wannan sai Allah.
Na biyu kuma shi ne, kada ka taɓa tunanin cewa dan ka yi wai dole sai an yi maka. Kai dai kawai ka yi dan Allah kuma dan kana ganin dacewar yin, ba wai dan sakayya ba. Sau tari wanda kake gwagwarmaya dan shi ma, zai iya zama mai zaginka. Wannan tabbas ne mu ganau ne ba jiyau ba. Amma ba komai ba ne, kai dai ka yi komai da kyakkyawar niyya kawai, wata rana za a gane cewa abin da kake yi ɗin nan yabo ya k**ata yi maka ba wai zagi ba. Za a iya wayar gari ma ana kewar ka idan an ji ka shiru alhalin ana ganin ga tarin abubuwa wanda da a ce kana nan da tuni ka yi iya yinka a kansu.
Sai abu na ƙarshe shi ne, kada ka taɓa zaton ka isa ka magance dukkan matsalolin al'umma, za ka yi ta yi amma ba za ka iya kaiwa ƙarshe ba. Kana rufe wannan ƙofar wata ce za ta bayyana, ka saka wa ranka salama ka yi iya abin da za ka iya yi. Mai iyawa gabaɗaya Allah ne kawai.
Ishaq Birniwa.
Secretary General,
BIRNIWA YOUTH INITIATIVES.