17/09/2026
SAKON TA’AZIYYA KAN ABIN DA YA FARU A M.I. WUSHISHI/LUKOTO
Cikin matuƙar jimami na samu labarin rasuwar mutanen da aka k**a a yayin samamen da aka gudanar kan masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a M.I. Wushishi/Lukoto.
Ina miƙa ta’aziyyata daga zuciya ga iyalai da ’yan uwan duk waɗanda s**a rasa rayukansu. Allah Ya jiƙansu, Ya gafarta musu, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsu, sannan Ya bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi. Ameen.
Yayin da NSCDC ta tabbatar da mutuwar wasu daga cikin waɗanda aka tsare tare da bayyana cewa ana gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar, rahotannin kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun nuna cewa adadin waɗanda s**a rasu na iya kasancewa ya fi adadin da aka tabbatar a hukumance.
Don haka, ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike cikin gaggawa, adalci da gaskiya, domin tabbatar da ainihin adadin waɗanda s**a rasu, gano musabbabin mutuwarsu, tare da ɗaukar matakin da ya dace idan an gano wani da ke da alhakin faruwar lamarin.
Haka kuma, a tabbatar an duba lafiyar waɗanda s**a tsira daga cikin mutanen da aka tsare, sannan a sanar da iyalansu gaskiya da wuri.
A wannan lokaci na alhini, abin da ya fi muhimmanci shi ne gaskiya, tausayi, adalci da kare rayuwar kowane ɗan Adam.
Hajarah Masaga Alhassan
’Yar Takarar NNPP Majalisar Dokoki ta Tarayya
Mazabar Chanchaga