Arewa Media Writers

Arewa Media Writers Arewa Media Writers Association is the mother association of all writers and social media organisations in northern Nigeria.
(1)

Kungiyar “Arewa Media Writers” Na Alhini Kan Rasuwar Janar Rabe Abubakar A Hannun Yan Kidnapping, Ta Kuma Yi Allah-Wadai...
13/06/2026

Kungiyar “Arewa Media Writers” Na Alhini Kan Rasuwar Janar Rabe Abubakar A Hannun Yan Kidnapping, Ta Kuma Yi Allah-Wadai Da Cigaba Da Tabarbarewar Tsaro

…Ƙungiyar ta ce mutuwar babban jami’in soja a hannun ’yan ta’adda babbar alama ce ta yadda matsalar tsaro ke ƙara tsananta, tare da kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa maimakon mayar da hankali kan abubuwan da ba su da muhimmanci.

Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr. Haidar H Hashim Kano, ta bayyana matuƙar alhini da damuwa kan rasuwar Janar Rabe Abubakar, wanda aka ruwaito ya rasa ransa a hannun yan ta’adda bayan gaza kubutar da shi da gwamnati ta yi.

Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan mummunan lamari ya sake bayyana irin girman ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta, inda har manyan jami’an tsaro ke rasa rayukansu duk da shekaru 35 da s**a kwashe suna yiwa kasarsu hidima.

A cewar ƙungiyar, hakan ya kamata ya zama abin da gwamnati da al’umma za su fi mayar da hankali a kai fiye da shagaltuwa da batutuwa marasa tasiri ga rayuwar jama’a.

“Arewa Media Writers” ta bayyana cewa ci gaba da irin waɗannan hare-hare na nuna akwai manyan gibi a tsarin tsaro da ke buƙatar a magance su cikin gaggawa.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa idan ba a ɗauki matakan da s**a dace ba, hakan na iya ƙara jefa al’umma cikin fargaba tare da barazana ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su sake nazari kan dabarun da ake amfani da su wajen yaƙi da ta’addanci, tare da samar da isassun kayan aiki, bayanan sirri da tallafin da jami’an tsaro ke buƙata domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

A cewar ƙungiyar, kare rayukan ’yan ƙasa da tabbatar da tsaro shi ne muhimmin nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati, kuma ya zama wajibi a ɗauki ƙarin matakai masu inganci domin dakile ayyukan masu aikata ta’addanci.

A ƙarshe, ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, rundunar tsaro da ɗaukacin ’yan Najeriya, tare da addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya ba iyalansa da ƙasa baki ɗaya ƙarfin jure wannan babban rashi.

Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Editor I Arewa Media Writers

Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Nuna Damuwar Ta Kan Sace Fiye Da Dalibai 600 A Cikin Shekaru Uku A Najeriya….Ƙungiyar ...
04/06/2026

Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Nuna Damuwar Ta Kan Sace Fiye Da Dalibai 600 A Cikin Shekaru Uku A Najeriya

….Ƙungiyar ta ce yawaitar sace ɗalibai duk da kuɗaɗen da aka ware domin tsaron makarantu na buƙatar sake duba dabarun tsaro a faɗin ƙasar nan.

Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”

Ƙungiyar "Arewa Media Writers" ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar na ƙasa Comr. Haidar H Hashim, ta bayyana matuƙar damuwa kan rahotannin da ke nuna cewa an sace fiye da ɗalibai 600 a sassa daban-daban na Najeriya cikin shekaru uku da s**a gabata.

Rahotannin sun nuna cewa an samu waɗannan hare-hare ne duk da cewa gwamnatin tarayya ta ware kimanin naira biliyan 145 domin aiwatar da shirye-shiryen inganta tsaro a makarantu da kare rayuka da dukiyoyin ɗalibai a faɗin ƙasar nan.

Ƙungiyar ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici musamman ganin yadda hare-haren ke ci gaba da jefa iyaye, malamai da ɗalibai cikin fargaba, tare da haifar da cikas ga harkar ilimi a wasu yankuna ƙasar.

A cewar ƙungiyar, ci gaba da sace ɗalibai na nuna cewa akwai buƙatar ƙarin matakai masu inganci wajen tabbatar da tsaron makarantu, musamman a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma, don haka wajibi ne gwamnati da hukumomin tsaro su tabbatar da cewa makarantu sun kasance wurare masu aminci ga ɗalibai da ma’aikatan ilimi.

"Arewa Media Writers" ta yi kira ga gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da dukkan hukumomin da abin ya shafa da su sake duba yadda ake aiwatar da shirye-shiryen tsaron makarantu domin tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware sun yi abin da ake bukata.

Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen dakile hare-haren masu garkuwa da mutane musamman yankunan arewacin Najeriya, tare da hukunta waɗanda s**a aikata irin waɗannan laifuffuka.

A ƙarshe, ƙungiyar ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro, iyaye da al’umma domin kawo ƙarshen matsalar sace ɗalibai da tabbatar da ingantaccen yanayin koyo a Najeriya.

Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Editor 1, Arewa Media Writers

Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Nuna Matuƙar Damuwa Kan Sace Ɗaliban Federal Polytechnic Kaura Namoda A Jihar Zamfara…...
03/06/2026

Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Nuna Matuƙar Damuwa Kan Sace Ɗaliban Federal Polytechnic Kaura Namoda A Jihar Zamfara

…Ƙungiyar ta ce cigaba da hare-haren ‘yan bindiga kan ɗalibai na barazana ga ilimi da zaman lafiyar al’umma a Arewacin Najeriya.

Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”

Ƙungiyar "Arewa Media Writers" karkashin jagorancin shugaban kungiyar na ƙasa Comr Haidar H Hashim, ta bayyana matuƙar damuwa da alhini kan rahotannin da ke nuna cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai guda bakwai na Federal Polytechnic Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun sace ɗaliban ne daga matsuguninsu da ke yankin Low-Cost a garin Kaura Namoda, lamarin da ya sake jefa iyayen ɗalibai da al’ummar yankin cikin fargaba da rashin tabbas.

Ƙungiyar ta bayyana wannan hari a matsayin wani babban abin takaici da ke nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a wasu sassan Arewacin Najeriya, musamman a wuraren da ya kamata ɗalibai su kasance cikin kwanciyar hankali suna gudanar da karatunsu.

A cewar ƙungiyar, yawaitar hare-haren da ake kaiwa makarantu da matsugunan ɗalibai na iya haifar da koma baya ga harkar ilimi, tare da kara tsoratar da iyaye daga tura ‘ya’yansu neman ilimi.

Ƙungiyar ta jaddada cewa akwai buƙatar jami’an tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin ceto ɗaliban da aka sace tare da tabbatar da kamo waɗanda s**a aikata wannan ɗanyen aiki, domin su fuskanci hukuncin da ya dace.

Haka kuma, "Arewa Media Writers" ta yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Zamfara da su ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro a cibiyoyin ilimi da matsugunan ɗalibai, domin hana sake aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Ya kare rayukan waɗanda aka sace, Ya ba jami’an tsaro nasarar ceto su cikin koshin lafiya, tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro.

Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Director, Media and Publicity I
"Arewa Media Writers"

Ƙungiyar "Arewa Media Writers" Ta Nuna Damuwar Ta Kan Durƙushewar Masana’antu 46 Dake Arewacin Najeriya...... Haka zalik...
01/06/2026

Ƙungiyar "Arewa Media Writers" Ta Nuna Damuwar Ta Kan Durƙushewar Masana’antu 46 Dake Arewacin Najeriya
...... Haka zalika ta kuma yi kira ga gwamnati tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki wajen dawo dasu

Ƙungiyar "Arewa Media Writers" ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar na ƙasa Comr. Haidar Hashim Kano, ta bayyana matuƙar damuwa kan yadda masana’antu da kamfanoni da dama da s**a kasance ginshiƙan tattalin arzikin Arewa s**a durƙushe s**a daina aiki gaba ɗaya cikin shekaru kaɗan.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce akalla masana’antu da kamfanoni 46 ne s**a rushe a jihohin Arewa, wanda hakan ya haifar da asarar dubban ayyukan yi tare da jefa al'umma da dama cikin mawuyacin hali.

Sanarwar ta bayyana cewa daga cikin kamfanonin da s**a durƙushe akwai Nigerian Paper Mill da ke Jebba, Lafiagi Sugar Company, Bacita Sugar Company, Northern Oil & Allied Kaduna, Kano Mattress Factory, Kano Plastic Company, Nigerian Bottling Company, Goldline Biscuit Factory, Arewa Metal Containers (AMECO), Kaduna Fertilizer Company, Peugeot Automobile Nigeria (PAN), United Nigerian Textiles (UNITEX), Nortex Textile, Funtua Textiles, Daura Textiles, Gombe Oil Mills, Ashaka Textile da sauran manyan masana’antun da s**a taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Arewa.

Ƙungiyar ta bayyana cewa waɗannan masana’antu sun kasance cibiyoyin samar da ayyukan yi ga dubban matasa tare da bunƙasa harkokin kasuwanci da masana’antu a yankin. Sai dai rushewar su ya haifar da ƙaruwar rashin aikin yi, talauci da koma bayan tattalin arziki a Arewa.

“Durƙushewar waɗannan masana’antu ba wai matsala ce ga Arewa kaɗai ba, illa ce ga tattalin arzikin Najeriya baki ɗaya. Lokaci ya yi da za a ɗauki matakin gaggawa domin farfaɗo da masana’antun da za a iya ceto su tare da samar da sababbi domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa,” in ji sanarwar kungiyar.

Haka kuma, ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin jihohin Arewa, masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen samar da hanyoyin dawo da martabar masana’antu a Arewa tare da ƙarfafa manufofin da za su taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa.

Ƙungiyar ta kuma jaddada buƙatar gudanar da cikakken bincike kan dalilan da s**a haddasa durƙushewar waɗannan masana’antu domin samar da mafita mai ɗorewa da za ta hana sake afkuwar irin wannan matsala a nan gaba.

A ƙarshe, kungiyar "Arewa Media Writers" ta yi kira ga shugabanni a kowane mataki da su fifita muradun al’umma, su mayar da hankali wajen gina tattalin arziki mai ɗorewa da zai amfani al’ummar Arewa da Najeriya baki ɗaya.

✍️ Comr. Muhammad Kwairi Waziri National Editor I, Arewa Media Writers

Rasuwar Alhaji Suleiman Abdulazeez Babban Rashi Ne Ga Arewa Da Najeriya Baki Ɗaya…Ƙungiyar ta bayyana marigayin a matsay...
20/05/2026

Rasuwar Alhaji Suleiman Abdulazeez Babban Rashi Ne Ga Arewa Da Najeriya Baki Ɗaya

…Ƙungiyar ta bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen mai kishin Arewa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare gaskiya, adalci da cigaban al’umma.

Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”

Ƙungiyar “Arewa Media Writers”, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr. Haidar H Hasheem, cikin matuƙar alhini da jimami take miƙa ta’aziyyarta bisa rasuwar Alhaji Suleiman Abdulazeez, ɗaya daga cikin waɗanda s**a assasa ƙungiyar Coalition of Northern Groups (CNG) Kuma kakakinta na farko.

Ƙungiyar ta bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga Arewa da Najeriya baki ɗaya, duba da irin gudummawar da ya bayar wajen kare muradun Arewa, yaƙi da jahilci, rashin adalci da kuma fafutukar tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa.

A cewar ƙungiyar, marigayi Suleiman Abdulazeez mutum ne mai tawali’u, sauƙin kai da kishin jama’a, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima ba tare da nuna son kai ko neman wata fa’ida ta ƙashin kansa ba.

Ƙungiyar ta ce marigayin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun muryoyin Arewa masu faɗin gaskiya, tare da tsayawa kan abubuwan da s**a shafi cigaban yankin Arewa da Najeriya baki ɗaya. Haka kuma ya kasance mai kishin ilimi da wayar da kai domin ceto matasa daga jahilci da talauci.

“Arewa Media Writers” ta ƙara da cewa rasuwar Alhaji Suleiman Abdulazeez ta haifar da babban gibi wanda zai yi wahalar cikewa, musamman ganin yadda ya kasance mai hikima, hangen nesa da kishin al’umma.

Ƙungiyar ta kuma miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, ƙungiyar CNG, masarautar Zazzau da ɗaukacin al’ummar Arewa bisa wannan babban rashi da aka yi.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya karɓi ayyukansa na alkhairi, Ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa, tare da bai wa iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.

✍️✍️
Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Editor 1, Arewa Media Writers

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Gargadi Gwamnatin Tarayya Da Jami'an Tsaro Kan Kisan Ƴan Arewa Da Suke Yi Wajen Kai Ha...
13/05/2026

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Gargadi Gwamnatin Tarayya Da Jami'an Tsaro Kan Kisan Ƴan Arewa Da Suke Yi Wajen Kai Hare-Hare Da Jiragen Yaki Da Sunan Kuskure

Ƙungiyar "Arewa Media Writers" karkashin jagorancin Comr Haidar Hashim Kano, ta bayyana matuƙar damuwar ta da takaici, bakin ciki kan yadda jinin al’ummar Arewa ke ci gaba da zuba ba dare ba rana, ta hanyoyin hare-haren ‘yan ta’adda da jiragen soji a jihohin Arewa.

Ƙungiyar ta ce abin ya fara wuce misali, domin a cikin kwanaki kaɗan jiragen sojin Najeriya sun kashe daruruwan mutane, ciki har da fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba, ga hare-haren yan ta'adda ga Boko Haram, wannan lamari yana ci gaba da zama abin takaici da gazawar gomnati da hukumomin tsaron kasar.

A cewar ƙungiyar, abin baƙin ciki ne yadda kullum Arewa ke tashi da labarin kai hare-hare, jikkata da ƙone rayukan al'umma, amma abin takaici shine yin shiru da gomnati keyi ba tare da yin bayani ba, babu isasshen jaje ga al'umma daga gomnati, babu kuma matakin da zau nuna cewa rayuwar talakan Arewa tana da daraja.

Ƙungiyar ta bayyana cewa shiru da ake yi bayan irin waɗannan manyan asara yana ƙara jefa al’umma cikin firgici da watsar da su kara zube a cikin ƙasa.

Ta kuma ce ba za a ci gaba da ɗaukar rayukan fararen hula a matsayin “kuskure” kawai ba tare da cikakken bincike da hukunci kan duk wanda ke da hannu ba, tana mai cewa jinin ɗan Arewa mai tsada ne.

Ƙungiyar ta yi kira da kakkausar murya ga Gwamnatin Tarayya da rundunar soji da su fito suyi bayani, su daina yin shiru, su daina ɓoye bayanai, su kuma ɗauki matakan gaggawa da za su kawo ƙarshen wannan kisan kiyashi da ke ci gaba da addabar yankin Arewa.

Ta ƙara da cewa lokaci ya yi da za a daina kallon Arewa a matsayin yankin da ake ci gaba da rasa rayuka ba tare da lissafi ba, tana mai cewa “idan jinin Arewa ya zama abin zubarwa ba dare ba rana, to ƙasa baki ɗaya tana cikin barazana.”

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi addu’a ga dukkan waɗanda s**a rasa rayukansu, tare da kira ga haɗin kai, gaskiya da kuma matakin gaggawa domin ceto sauran rayukan da s**a rage.

Hoto: Muhasa Radio

✍️✍️Muhammad Kwairi Waziri
National Editorial 1, Arewa Media Writers

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Yi Allah-Wadai Da Ci Gaba Da Hare-Haren Jiragen Yaƙi A Yankin ArewaƘungiyar Arewa Medi...
10/05/2026

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Yi Allah-Wadai Da Ci Gaba Da Hare-Haren Jiragen Yaƙi A Yankin Arewa

Ƙungiyar Arewa Media Writers ƙarƙashin jagorancin Comr. Haidar Hashim Kano, ta sake bayyana matuƙar damuwa tare da Allah-wadai kan rahotannin wani sabon harin jirgin yaƙin sojin saman Najeriya da ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a matsugunan Guradnayi da ke kusa da garin Kasasu a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce abin takaici ne yadda irin wannan lamari ke ci gaba da faruwa a sassa daban-daban na Arewa, duk da rahotannin makamantan hare-hare da s**a faru a baya ba tare da samun cikakken bayani ko matakin da ya dace daga hukumomi ba.

Ƙungiyar ta bayyana cewa har yanzu ba a ga wani bayyanannen mataki ko bayani daga gwamnati da hukumomin tsaro kan irin waɗannan abubuwa da ke haddasa asarar rayukan fararen hula ba, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin al’umma da kuma rage amincewa da tsarin kare rayuka da dukiyoyi.

Sanarwar ta ƙara da cewa ci gaba da faruwar irin waɗannan hare-hare a jere na nuna bukatar gaggauta sake duba dabarun gudanar da ayyukan tsaro, musamman wajen tabbatar da sahihin bayanin sirri kafin kai farmaki a wuraren da ke da yawan jama’a.

“Wannan ba shi ne karo na farko ba, kuma rashin ɗaukar mataki kan irin abubuwan da s**a gabata ya ƙara haifar da sabon tashin hankali da rashin tabbas a zukatan al’umma,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da rundunar sojin Najeriya da su fito fili su yi bayani ga jama’a tare da gaggauta gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin, domin tabbatar da adalci da hana sake aukuwar irin wannan kuskure a nan gaba.

Haka kuma ta jaddada cewa kare rayukan fararen hula wajibi ne a kowane hali, kuma dole ne a tabbatar da cewa duk wani aiki na tsaro yana tafiya cikin tsari da bin ƙa’ida.

A ƙarshe, Arewa Media Writers ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda s**a rasa rayukansu tare da addu’ar Allah ya jikansu da rahama, ya kuma bai wa waɗanda s**a jikkata lafiya cikin gaggawa.

Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Editor I, Arewa Media Writers

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Soki Gomnati Tarayya Kan Sabon Harin Da Ƴan Ta'adda S**a Kai Yau A Jiƙamshi A Jihar Ka...
04/05/2026

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Soki Gomnati Tarayya Kan Sabon Harin Da Ƴan Ta'adda S**a Kai Yau A Jiƙamshi A Jihar Katsina

Ƙungiyar Arewa Media Writers ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar na ƙasa Comr. Haidar H Hasheem ta bayyana matuƙar damuwa tare da Allah-wadai kan harin da yan bindiga s**a kai yau a garin Jiƙamshi da ke jihar Katsina, wanda ya yi sanadin rasa rayuka tare da jikkata wasu mazauna yankin.

A cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta ce wannan sabon hari ya ƙara nuna irin tsananin matsalar tsaro da ke ci gaba da addabar wasu sassan Arewacin Najeriya, inda al’umma ke ci gaba da fuskantar barazanar rashin tsaro a kullum.

Ƙungiyar ta ce: “mu yi haƙuri mu faɗi gaskiya, abin da ke faruwa a fannin tsaro yana buƙatar ɗaukar matakin gaggawa da sabbin dabaru domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”

Sanarwar ta ƙara da cewa dole ne a ƙara ƙaimi da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da al’umma domin dakile irin waɗannan hare-hare, tare da tabbatar da cewa an kawo ƙarshen zubar da jini da ke faruwa a yankunan karkara.

Ƙungiyar ta kuma mika saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda s**a rasa rayukansu, tare da addu’ar Allah Ya jiƙansu, Ya kuma bai wa waɗanda s**a jikkata sauƙin jinya.

A ƙarshe, ta jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban nauyin gwamnati, don haka akwai bukatar a ɗauki matakai masu ƙarfi da inganci don dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Editor I, Arewa Media Writers

Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Soki Gwamnatin Tarayya Kan Amfani Da Kotu Da Hukumomi Wajen Rusa Jam’iyyun AdawaƘungiy...
29/04/2026

Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Soki Gwamnatin Tarayya Kan Amfani Da Kotu Da Hukumomi Wajen Rusa Jam’iyyun Adawa

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” ƙarƙashin jagorancin Comr Haidar Hashim Kano, ta bayyana matuƙar damuwa tare da Allah-wadai da yadda ake zargin Gwamnatin Tarayya da amfani da kotuna da wasu hukumomi domin takura wa jam’iyyun adawa a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce irin wannan mataki na barazana ga ginshiƙan dimokuraɗiyya, domin kuwa adawa na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da daidaito, gaskiya da kuma duba ayyukan gwamnati.

Ƙungiyar ta jaddada cewa amfani da bangaren shari’a da hukumomin gwamnati wajen murkushe jam’iyyun adawa na nuna karkacewar tafiyar dimokuraɗiyya, tare da rage amincewar jama’a ga tsarin mulki.

“Abin takaici ne yadda ake amfani da kotuna da wasu hukumomi domin raunana jam’iyyun adawa, maimakon a bar su su gudanar da harkokinsu cikin ‘yanci da gaskiya,” in ji sanarwar.

Haka kuma, ƙungiyar ta bayyana cewa irin waɗannan matakai na iya haifar da rashin zaman lafiya da kuma tada hankalin al’umma, musamman idan aka ci gaba da tauye ‘yancin siyasa.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa dimokuraɗiyya ba za ta bunƙasa ba sai an tabbatar da adalci da kuma bai wa kowane ɓangare dama iri ɗaya a fagen siyasa.

Don haka, “Arewa Media Writers” ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta guji amfani da hukumomi da kotuna wajen cimma manufofin siyasa, tare da mutunta dokokin ƙasa da ‘yancin kowa.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga al’umma da su kasance masu lura tare da kare haƙƙoƙinsu ta hanyoyin da s**a dace.

Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Editor I, Arewa Media Writers

Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Yi Allah-Wadai da Amincewa Da Sabon Bashin Dala Miliyan 516.3 Domin Aikin Titin Sokoto...
28/04/2026

Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Yi Allah-Wadai da Amincewa Da Sabon Bashin Dala Miliyan 516.3 Domin Aikin Titin Sokoto–Badagry

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” ƙarƙashin jagorancin Comr Haidar Hashim Kano, ta yi Allah-wadai da matakin da Majalisar Wakilai ta ɗauka na amincewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓo bashin dala miliyan 516.3 domin aikin titin Sokoto–Badagry.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce wannan mataki na ƙara ɗora wa ƙasar nan nauyin bashi a daidai lokacin da tattalin arziƙin al’umma ke cikin mawuyacin hali, abin da ke haifar da damuwa kan makomar tattalin arziƙin Najeriya.

Ƙungiyar ta jaddada cewa yawan karɓar bashi ba tare da cikakken bayani kan hanyoyin biyan sa da kuma tasirin sa ga rayuwar al’umma ba na nuna rashin tsari da hangen nesa daga bangaren gwamnati da majalisun dokoki.

“Abin takaici ne yadda ake ci gaba da ɗaukar irin waɗannan matakai ba tare da la’akari da halin ƙunci da talauci da al’umma ke ciki ba. Wannan na ƙara tsananta wahalhalun da jama’a ke fuskanta a yau,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda Majalisar Dattawa ta amince da irin waɗannan shirye-shirye ba tare da zurfin nazari da la’akari da ra’ayin al’umma ba, lamarin da ta ce bai dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.

Ta ƙara da cewa ci gaba da jingina ci gaban ƙasa da bashin ƙasashen waje na iya jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziƙi a nan gaba, tare da barazana ga ‘yancin tattalin arziƙin ƙasar.

Don haka, “Arewa Media Writers” ta bukaci Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dattawa da su sake nazari kan wannan mataki, su fifita hanyoyin inganta tattalin arziƙi cikin gida ba tare da dogaro da bashin waje ba.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da irin waɗannan matakai tare da riƙe shugabanni da alhakin duk wata doka ko shawara da za ta shafi rayuwarsu.

Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Editor I, Arewa Media Writers

Address

Abuja
Abuja

Telephone

+2349030357049

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Media Writers posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Arewa Media Writers:

Share