16/05/2026
Nous (La Sous-Commission nationale de la langue Hausa / Burkina) avons procédé, ce vendredi 15 mai 2026 à la Bibliothèque nationale du Burkina, au lancement officiel de l’initiative pour la promotion et la valorisation du patrimoine culturel Hausa.
Portée en collaboration avec l’association Makaranta et avec l’accompagnement du ministère en charge de la Culture, notre initiative ambitionne de renforcer la visibilité, la transmission et la préservation des valeurs culturelles Hausa au Burkina Faso. Elle vise notamment à promouvoir les savoirs, traditions, langues, arts, pratiques et expressions culturelles Hausa dans la vie quotidienne et dans l’espace national.
La cérémonie a connu plusieurs temps forts, notamment la présentation de l’emblème de la culture Hausa, une exposition d’objets et d’éléments culturels ainsi qu’une dégustation de mets traditionnels Hausa
et la désignation des points focaux représentants de la culture Hausa dans les différentes régions du Burkina.
Mu (Hukumar Hausa ta Kasa/ Burkina) mun gudanar da bikin ƙaddamar da shirin bunƙasa da inganta al’adun Hausawa a hukumance, a wannan Juma’a 15 ga watan Mayu 2026, a ɗakin karatu na ƙasa na Burkina.
An gudanar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Makaranta da kuma goyon bayan ma’aikatar kula da al’adu. Manufar wannan shiri ita ce ƙara fito da al’adun Hausawa fili, tabbatar da ci gaba da wanzuwarsu da kuma kiyaye su a Burkina Faso. Haka kuma, shirin na da burin bunƙasa ilimi, al’adu, harshe, fasaha, dabi’u da sauran al’adun Hausawa a rayuwar yau da kullum da kuma a faɗin ƙasa baki ɗaya.
Bikin ƙaddamarwar ya ƙunshi muhimman abubuwa da dama, ciki har da gabatar da tambarin al’adun Hausawa, baje kolin kayayyaki da al’adun Hausawa, tare da ɗanɗana abincin gargajiyar Hausawa da kuma naɗin wakilan cibiyoyin hulɗa na al’adun Hausawa a yankuna daban-daban na Burkina Faso.